✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudi na 5: Yin Ladabi ga Shugabancin Maigida 4

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, Ga cigaban bayanin matsayi da girman miji daga inda muka tsaya satin da ya wuce; wannan…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, Ga cigaban bayanin matsayi da girman miji daga inda muka tsaya satin da ya wuce; wannan tunatarwa dai mun sameta ne a kafafen sada zumunci na yanar gizo ba tare da sunan marubuci ko marubuciyarsa ba. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar, amin

Wane ne miji 2
Aljanna wani sai ya yi yaki an kashe shi zai samu, wani sai ya yi shahada, wani sai ya yi aiki na shekaru bila adadin, wani ma ba zai samu ba! Ke kuma sai aka ce miki aljanna tana karkashin kafar mijinki!
Da a ce miki je ki samo abu kaza a wuri kaza, watau an sanar dake inda yake kenan; da kuma a ce maki je ki samo kaza a duk inda za ki samo shi, watau ba sanar da ke wajen ba, wanne ya fi?
Ko wa zai ce zai je ya nemo a wurin da yake sananne, komai wahalar daukar kuwa, tunda in ka dauka ka dauka kenan, wancan kuwa kina iya nemo wa kafin ki kawo ya subuce ko ya bata, sai kin sake nemowa kuma.
Aljanna kike nema bayin Allah suna zuwa su yi bautar shekara saba’in don dacewa da aljanna, Ke kuma fah? In mijinki ya bata miki rai sai ki kalli ni’imar da Allah ya yi miki ta hanyar aure kafin ki fara nadamar aure, don nadamar da yin wasu abubuwa da ba su dace ba yin butulci ne ga Allah! Komai ya same ki me dadi ko mara dadi ki gode wa Allah!
Allah Yana cewa: “In kuka gode Min sai in kara maku (ni’ima) in kuma kuka bijire Min/kafirce Min (kuka ki gode Min, kuka raina abinda Na yi muku), to azabaTa me tsanani ce!” Azabar Allah za ki zaba ko biyayyar miji?
In kika duba ni’imar da rufin asirin da aure ya yi miki, tun daga ranar da aka daura aure an maida ke fa sabuwa kamar yau aka haife ki, an yaye miki zunubanki na baya da kika yi saboda darajar aure. Kuma ko me kika yi a gidan mijinki lada ne, ki yi kwalliya lada, ki yi shara lada, k iyi girki lada, komai kika yi lada ne duk da amfanin kanki ne, in yaranki kike kula da su lada ne!
Allah Yana sonmu Yana so mu rabauta, komai ya tsara mana don dai mu tsira mu ji dadi. Amma me? Mata suna yawan  bijirewa Allah, ku fada min me ya sa mata ba za su fi yawa a wuta ba?
Komai Allah ya yi mana, amma mun fi son bin son rai da zuciya, mun watsar da bin Allah! Da ki yi sallah a masallaci fa gara ki yi sallah a kuryar dakinkin in akwai  lungu a dakin ma to ya fi maki lada da karbuwa a wajen Allah!
Don a nuna maki Allah ma ya fi so ki bauta maSa a cikin dakinki, don ba inda ya kai miki wannan dakin daraja. Musulunci ya gatanta mata nesa na kusa ba, amma suna bari maza na yi musu wayo, suna mana rashin kirki muna ramawa muna biye musu, to yin haka biyu babu ne sakamakon shi, kin zubar da kai a wurin miji kuma ki je lahira ki ji jiki, wa ya yi asara kenan?
Rayuwar dai duk aljanna ake yi wa, ya za a yi a tsira? Don nan dai ba shi ne madawwama ba, can din shi ne gaskiya, to yaya za ki yi a can din ki samu wuri mai kyau? Abin da za ki kalla kenan. Kawai komai ki yi shi tsakaninki da Allah, ba a ce komai ki zauna a cuce ki ba amma, akwai hanyar lalamar zartar da komai.
In kuma an cuceki din koda kuwa ajalinki hakan ya yi, ba ki fadi ba, In ka yi komai don Allah  ko ba ka ga amfaninsa ba a nan to ka jira babban rabo, domin lallai Allah ba Ya karya alkawari, tun da Ya ce Zai yi,  Zai yi, ba Zai bar ki ba. Kar ki ce wai kina ta wahala amma shiru, kowa akwai irin yadda
Allah Ya tsara masa rayuwa, wasu a nan za su ji dadi, wasu a can, wasu kuma duka nan da can din, kuma ba a ce wa Allah don me? Domin Shi mai yin abin da Ya so ne!
Mu tsayar da imani.  Biyayyar miji a cikin biyayyar Allah take.   In kika ci mutuncin miji, ke ma kin san wa kika yi wa, don idan Mahaifinki ya kawo mai gadi ya ce ki bis hi, ki yi mai biyayya in kin wulakanta maigadin nan hakan na nuna raina babanki kika yi kuma kin nuna bai isa ba!
To uba ma kenan, ina kuma ga Allah da ba zai yiwu a kwatanta Shi da wannan abubuwan ba?  Mu kiyaye iyakokin Allah! Don wallahi Allah abin tsoro ne ko ba don wutarSa ba, Allah tun a duniya ba yadda ba Zai iya yi da mutum ba!
 Da fatan Allah Ya ganar da mu duka.  Ya dora mu akan hanya madaidaciya, amin.
Sai sati na gaba in sha Allah.   Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.