Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani daga inda muka kwana a makon jiya.
Hanyoyin Tafiyar Da Kunyar Ibadar Aure; cigaba…
In kuma yanayin halayyarta ne, tunanin ta ko irin siffar jikinta ke sa tana jin kunya, sai ta fara aikin kawar ko canza wannan tunanin ko halayyar, misali in tana ganin kanta a matsayin marar sha’awa dole ta kankare wannan tunanin, kamar yadda na sha fada, ba macen da ba ta da sha’awa illa dai yanayin tunaninmu ke ba mu irin sha’awar da muke da ita. In kuma tana tunanin ba ta da sha’awa don ba ta da siffar jiki iri kaza ko don ba ta mallaki wani abin ba, dole sai ta canza wannan tunanin domin siffa ba ita ke ba da sha’awa ba, sha’awa shauki ce da ke cikin zuciya, ba ta da dangantaka da siffar jiki ko kadan amma tana da dangantaka da irin tunanin cikin zuciyarmu game da ita.
Dole dai sai uwargida ta fitar da duk wani karkataccen tunanin da take da shi ko ta yi riko da shi game da yanayin sha’awarta; ta tabbatar wa kan ta da ita cikakkiyar mace ce ta kowane fanni, ta tabbatar wa kanta ita mai sha’awa ce, kuma sha’awar ma cikakkiya, zazzaka kuma kayatacciyar sha’awa! Ta yadda kuma ta amince da wannan har cikin zuciyarta domin haka din shi ne gaskiya kuma shi ne daidai.
Sannan duk wani jin kai da tsoron bayyanar da rauni ga maigida, wannan ma dole ta a je shi gefe guda, shimfidar aure, in mun lura da yanayinta, waje ne na jin zuciya da jin jiki ba ‘jin kai’ ba. Don haka in dai har uwargida na so sha’awarta ta bude, dole sai ta rika aje jin kan ta a gefe in za ta kusanci shimfidar aurenta, domin in tana ji a kanta, to fa ba za ta ji komai a kafafen jin sha’awa ba, su ne: zuciya, ruhi da jikinta.
Uwargida: Horon Sha’awa:
Sannan uwargida ta fara horar da kanta don ganin ta koyi baza fasahohin macentakarta ga maigidanta, musamman ga wacce kunya ta zama wani babban yanki na daga halayyarta; sai ta zauna a gaban madubi ta rika koyar da kan ta ’yan abubuwan kwarkwasa da za ta rika yi wa mijin, ta yadda in ta saba ta kuma kware da yin su, to a hankali nauyi da jin kunyar yin su gaban maigida zai ragu, don wata sa’in ‘ban iya ba, da ban san yadda ake yi ba’ na daya daga cikin abin da ke sa yawanci matan aure jin kunyar yin abubuwan nuna kauna ga mazajensu. Don haka sai uwargida ta yi wa kanta horo na musamma yadda za ta rika yin murmushin sha’awa, murguda baki cikin shagwaba; daga gira da fari da ido, kallon so da kauna; lumshe ido; ta rika koyon yadda za ta rika sarrafa da kashe muryarta don jan ra’ayin maigida, in ma da hali sai ta rika daukar sautin muryarta a rikodar wayarta tana jin yadda banbancin caccanzawar muryarta, har sai ta ji ta kware sosai. Ta horar da kanta wajen yin tafiya cikin kwarkwasa da yanga da ’yan murgude-murgude.
Sai kuma ta koyi sa kaya, musamman kayan bacci masu laushi da shara-shara, domin suna taimakawa wajen kara motso da karfi da kaifin macentaka, wadanda bayyanuwar su na kawo karuwar jin dadi da natsuwa a zuciyar uwargida, wadannan kuma su ne sinadarai biyu da ke balle kofofin sha’awar uwargida har su sa sha’awa ta tumbatsa.
Sannan in akwai wata kyama ta daban a zuciyar uwargida game da ibadar aure, yanayin gabatarwa ko kyamar shi maigidan, to wannan ma na iya danne mata sha’awa, Don haka dole dai ta san hanyar share wannan kyamar, hanya mafi sauki ita ce in ta tuna abin da wannan kyamar ke tare mata ya fi muhimmanci a gare ta sama da ta yi ta ajiyar kyamar nan cikin zuciyarta, domin dai, kyama irin ta zuci ba ta da wani amfani ga rayuwar dan adam in ban da ta tare masa wasu abubuwan da ka iya zama alfanu a rayuwar sa.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba in Allah Ya kai mu, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.