✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan kotu za su koma aiki makon gobe — Gwamnatin Tarayya

An yaba wa dukkanin bangarorin kan yadda suka cimma matsayar.

Gwamnatin Tarayya ta ce daga makon gobe kotuna da majalisun jihohin kasar nan za su koma bakin aiki bayan yajin aikin da kungiyoyin Ma’aikatan Shari’a, JUSUN, da na Majalisun Jihohi, PASAN suka shiga.

Kungiyoyin biyu sun shiga yajin aikin ne sakamakon kememe da gwamnoni suka yi na rashin aiwatar da dokar cin gashin kan kudaden bangaren shari’a da na majalisun jihohin.

Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige ne ya bayyana haka a Abuja ranar Juma’a, bayan ganawar da bangaren gwamnati da na masu yajin aikin domin warware takaddama kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna da aka cimma a ranar 20 ga watan Mayu.

Da yake jawabi kan sakamakon ganawar, Ngige, ya ce dukkanin gwamnoni 36 bisa jagorancin Shugaban Majalisarsu, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da Mataimakinsa Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato, sun rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar da aka cimma ranar 20 ga watan jiya a madadin takwarorinsu.

A cewar Ministan, bisa abin da suka cimma wa a wajen taron, ana sa ran kotuna da Majalisun Jihohin za su koma bakin aiki a makon gobe. 

Mataimakin Shugaban JUSUN, Kwamred Emmanuel Abisoye ya gode wa ministan bisa kokarinsa na warware kiki-kakar, don haka yana fatan dukkanin bangarorin za su cika alkawuran da suka dauka.

Shi ma Shugaban Kungiyar PASAN, Kwamred Mohammed Usman ya bayyana fatan dukkan masu ruwa da tsakin za su yi abin da ya dace domin ganin ma’aikatan majalisun sun koma bakin aiki.

A nashi bangaren, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, Kwamred Ayuba Wabba ya yaba wa dukkanin bangarorin kan yadda suka cimma matsayar.