✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata 3,057 na amfani da takardun bogi a Neja

Ma'aikata 3,051 na aka gano suna amfani da takardun shaidar karatu na bogi a Jihar Neja

Kwamitin binciken albashin ma’aikatan na Jihar Neja ya gano maaikata 3,051 da suka shiga aiki da takardun makaranta na bogi.

Shugaban kwamitin da ke tantance ma’aikatan jihar, Ibrahim Panti, wanda shi ne Kwamishinan Ayyuka na jihar ya ce daga cikin sunaye 26,387 da Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar ya tura wa kwamitin, ma’aikata 20,675 kadai aka tantance.

Wasu 3,057 kuma na da matsalaloli da suka danganci shiga da takardun makaranta na jabu.

Panti ce mutum 25,861 ne kadai daga cikin ma’aikata 26,387 da aka ba kwamitin sunayensu, suka yi rajista a shafin kwamitin na intanet, yayin da har yanzu wasu 1,789 ba su kammala ba.

Ya kara da cewa ma’aikata 773 ba su gabatar da kansu ba domin tantancewa, sai 340 da suka mutu ko suka yi ritaya daga aiki.

Kwamishinan ya ce har yanzu shafin intanet din kwamitin a bude yake ga ma’aikatan ba su yi rajista ba, kuma ana jiran wadanda ba a tantance ba su zo domin a tantance su.

Ya kuma gargadi wadanda ba a tantance ba da su gaggauta gabatar da kansu kafin a rufe aikin tantancewar gwamnati ta dauki mataki a kansu.