✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin tambayoyi Da gaske ne akwai shekarun da mai ciwon sikila zai kai ya samu raguwar kaifin ciwon? Ni da ba na samun matsala sosai…

Amsoshin tambayoyi

Da gaske ne akwai shekarun da mai ciwon sikila zai kai ya samu raguwar kaifin ciwon? Ni da ba na samun matsala sosai amma a yanzu ina yawan samun ciwon hakarkari

Daga SS Adamu, Katsina

 

Amsa: Eh, kuma a’a. Amsar tana da kunne biyu. Da yawan masu ciwon sikila sun fi shan wahala suna yara, saboda yarinta da raunin garkuwar jiki, amma idan suka fara girma sai abin ya fara sauki. Wadansu kalilan kuma kamarka sai sun kai wani munzali na shekaru abin ya fi kamari, amma wannan yawanci akwai dalilai. Misali dalili na matsin tattalin arziki ko canjin wurin zama. Idan yaro mai sikila ya taso gidansu da gata, ba zai sha wahala sosai ba kamar na wanda gidansu ba gata sosai, to amma idan gatan ya ja baya, ko ya canja wurin zama kamar ya tafi makarantar kwana, za a ga alamun tashin ciwon yana karuwa. Ka ga ke nan ba wai daga ciwon ba ne, a’a daga yanayin da mutum ya samu kansa a ciki ne. Saboda haka ka duba ka ga wane yanayi naka ne ya canja da ya sa kake yawan samun ciwon hakarkari a yanzu, idan zai yiwu ka magance shi.

 

Da na ji ana cewa idan mace na samun ciwon mara lokutan al’ada wai zai kasance akwai matsala wajen samun haihuwa. Ko haka ne?

Daga Ummu Malik

 

Amsa: A’a ba gaskiya ba ne, shaci fadi ne. Daga sunanki ma za a iya hasashen cewa ke babar Malik ce. Idan kina samun ciwon mara lokacin al’ada, da a lokacin da za ki haifi Malik da kin samu matsala.

 

An yi wa mai dakina aiki an ciro ’yan tagwaye. Kamar mako nawa aikin yake kafin ya warke gaba daya?

Daga Umar Muhammad

 

Amsa:Ai da ka yi wa likitocin nata wannan tambaya. Duk da cewa ana sallama kafin wurin da aka yi dinkin ya warke, ba ana nufin shi ke nan ba za a kula da shi ba. Daga ranar da aka yi tiyatar akan samu a kalla mako shida zuwa takwas kafin a ce aikin ya warke wurin sosai ya yi kwari. Amma wannan ya danganta da yadda aka kula da ciwon ke nan don ganin cewa ciwon bai samu wata matsala ta shigar kwayoyin cuta ko ta tsinkewar zaren tiyata ba. Kafin a yi sallama ma’aikatan jinya sukan yi bayanin abin da ya kamata a rika shafawa wurin domin ya yi saurin warkewa ba tare da wasu matsaloli ba. Yawanci sukan ce a rika shafa man shanshan-bale, wato gentian biolet ko man spirit a kullum kamar sau uku a rana ko ma fiye, ko ma a rika zuwa duk bayan ’yan kwanaki asibiti ana wanke wurin.