Shin sayen magani a kyamis har ma a zo ana yi wa mutum allura ko karin ruwa ba ya da illa kuwa?
Daga Yusuf M.K
Amsa: Eh kwarai akwai illa, dama sayen magani kawai ake so a rika yi a kyamis ba allura da karin ruwa ba. Domin kyamis ba zai maye gurbin asibiti ba. Su ma’aikatan kyamis din iri biyu ne, akwai masu ilimin magani na digiri masu lasisi, wadanda za su iya rubutawa da sayar da kowane irin magani ne a duniya, akwai kuma wadanda aka ba horo na musamman kawai a kan sayar da kananan magunguna kamar na ciwon kai da mura da tari. Su wadannan ba su da lasisi, kuma ba sa rubuta magani sai dai idan an kawo musu takardar likita su duba maganin su bayar idan akwai. Yawanci ma a ido mutum zai iya bambance kyamis din da yake da kwararre (Pharmacist) da wanda ba na kwararre ba, wadanda ake kira ‘Patent Medicine Store.’ Domin na kwararre ya fi na wanda ba kwararre ba tsari da shiryuwa da haduwa.
To a shi inda ake da kwararren ma’aikaci mutum zai iya zuwa ya fadi matsalolinsa shi kwararren ya ba shi shawarwari har ma da wasu magunguna idan ta kama, amma ba zai yi jinya ba, wato ba zai yi allura ko karin ruwa ko tiyata ko kwantarwa ba, tunda ba huruminsa ba ne. Idan aka ga ana yin jinya a kyamis, to a san kuskure ne babba wanda idan aka kama wurin za a iya kulle mai shi a kuma ci tararsa. Ka ga ke nan ba za a iya zuwa kyamis a mayar da shi kamar asibiti ba. Domin sam ba tsarinsu daya ba.
Hukumomin lafiya na kasa kamar na PHCDA sun zayyana abin da wurin jinya ya kamata a ce yana da shi, komai kankantarsa ya hada da wurin sayar da magani (kuma ya kasance akwai magungunan, ba wai hoto ba), da kwararren mai magani zai zauna a ciki, da likita ko makamancinsa kamar malamin lafiya na CHEW da ma’aikacin jinya wato nas, sai ungozoma, sai dakunan duba marasa lafiya da dakunan jinya (ba dole sai na kwanciya ba) da isasshen ruwa da wuta da bayan gida da dakunan gasa kayan aiki da tsabtace su da wurin kona shara da katon allon mai sunan wurin da alama da sauransu. Wato ke nan duk wurin da ka ga mutum daya ya hada wadannan ayyuka duka shi kadai yana aiki (shi ne masanin magani, shi ne likita, shi ne mai jinya, a wasu lokuta ma don ganganci har tiyata suke) to a guje shi, domin barna da nakasa mutane kawai za a yi, ba sama musu lafiya ba. A inda ma aka samar da wadancan ma’aikata dole sai an yi taka-tsantsan an tantance wane ne kwararre wane ne mabarnaci.
Shin idan mutum yana rayuwa da mai ciwon kanjamau kuma suna amfani da kayan gida tare, zai iya dauka?
Daga Atamma Anthony, Nassarawa
Amsa: A’a babu wata damuwa domin babu labarin wanda ya dauki ciwon kawai domin ana zaune a gida daya da mai ciwon ko ana amfani da kayan gida daya da mai ciwon. A kimiyyance ma sai dai idan akwai alaka ta kut-da-kut (kamar saduwa ko amfani da reza daya ko allura) a tsakanin mai ciwon da marar ciwon.
Mutumin da likita ya hana shan man gyada zai iya shan wani kamar kwantirola?
Daga Dauda Mani
Amsa: Mutumin da likita ya hana shan man gyada sai ya tambayi likitan to wane zai sha. Ka ga shi ke nan mu ba mu shiga hurumin likitansa ba, shi kuma zai fi samun fa’idar abin da ya sa aka hana shi cin man gyadar.
Ni ne duk lokacin da na yi rauni babba ko karami to idan wurin ya warke tabon ma sai ya rika girma yana kaikayi. To abin na damuna. Ko akwai magani?
Daga Yahya Garba, Gobir
Amsa: Eh, wannan alamar wani ciwon fata ne da mukan kira hypertrophic scar, wato duk wanda ya ji ciwo sai tabon ya yi ta girma a wani lokaci ya zama kamar tsiro. Akwai magunguna na shafawa har da allurai, wadanda in ka je babban asibiti bangaren tiyata ko na fata da yake Gobirawa na da son tsagu za a ga masu irin wannan matsala sukan nuna alamun ciwon a wurin tsagun, inda tsagun za su yi kumburi suntum-suntum maimakon rami.
Idan na gama fitsari na dawo bayan wani dan lokaci sai na ji wani yana zuba a wando. Mene ne haka? Mene ne magani?
Daga Bashari Gwagwa
Amsa: Eh, wannan ma wata alama ce da a likitance muke kira terminal dribbling wato tsiyayar fitsari ko digar fitsari bayan an dauka cewa an gama. Kuma mu mun fi alakanta shi da shigar kwayoyin cutar mafitsara ko ciwon kumburin prostate, wata ’yar halitta a karkashin marar maza. To tunda a nan ba za a san wane ne ba a ciki, sai dai ka je likita ya tantance maka.
Shin mene ne maganin ciwon karkatan (wato rawar hannu)?
Daga Joshua Kago
Amsa: A likitance cututtuka da dama za su iya sa rawar hannu, tun daga matsalolin kwakwalwa zuwa na lakar gadon baya, zuwa na hadarin abin hawa zuwa wasu kwayoyin magunguna na asibiti da ma kwayoyi masu bugarwa da yawan shan barasa da ciwon hanta, duk za su iya sa rawar hannu. Don haka mai wannan matsala sai ya je an duba shi an ga wanne ne a ciki ya kawo rawar hannun kafin a ba shi magani, domin kowane da aka zayyana maganinsa daban.