✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama Aku 73 da aka yi fasa-kwaurinsu

Hukumar Kwastam da hadin gwiwa da ta Tabbatar da bin Dokokin Muhalli ta kasa (NESREA) ta mika wa Gidauniyar Adana Kayayyaki ta Najeriya (NCF) wasu…

Hukumar Kwastam da hadin gwiwa da ta Tabbatar da bin Dokokin Muhalli ta kasa (NESREA) ta mika wa Gidauniyar Adana Kayayyaki ta Najeriya (NCF) wasu Aku 73 da ta kama an shigo da su ba bisa ka’ida ba.

Akun dai an mika su ga Gidauniyar ne a gidan adaan namun dajin Kano, domin mika su kudancin Najeriya in da aka shigo da su.

A baya ma dai Hukumar Kwastam din shiyyar jihar Kano da Jigawa, ta ce ta kama wasu guda 99 ranar 21-Yuni, in da ta mika su ga NESREA domin adana su a gidan Zoo da ke Kano.

Yayin da yake karbar Akun, Babban Daraktan Hukumar (NCF) Dokta Muntari Aminu-Kano, ya tabbatarwa Kwastam din cewa za su kula da Akun yadda ya kamata, kafin sakinsu a dajin Kudancin Najeriya.

“Muna da gidan adana namun dajin da ya dace da nau’in Akun  a jihar Legas, kuma za mu tabbatar da mun farfado da su bayan shan wahala a hannun wadanda suka shigo da su ba bisa ka`ida ba, har gashinsu ya kade”

“Da sun warware za mu sake su a daji in da za su iya rayuwa,” inji shi.

A nasa bangaren Abdulrahem Mudashir wanda ya wakilci Babban Daraktan NESREA ya bayyana gamsuwarsa da kalaman Dokta Muntari, tare da yabawa Hukumar Kwastam din da gidan namun dajin Kano, bisa kama Tsuntsayen da kokarin ceton rayuwarsu.