Alkaluman masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya na ci gaba da raguwa a cikin kwanaki hudu a jere.
Hakan na zuwa ne yayin da masu cutar suka haura 16,000 a jihohi 35 ba babban birnin kasar , Abuja.
Daga Alhamis 11 zuwa Lahadi 14 ga watan Yuni sabbin masu harbuwa da cutar sun yi ta raguwa daga 681 zuwa 403.
A dan tsakanin ne kuma wadanda suka warke suka kai mutum 5,220 bayan an sallami karin wasu 726 da suka warke daga cutar a Najeriya inda mutum 16,085 suka taba harbuwa ita.
- Za mu sake rufe wuraren ibada idan… —Mustapha
- Masu coronavirus a Najeriya sun haura 15,000
- ‘Coronavirus ta kashe mutum 587 a Kano cikin mako biyar’
Sai dai kuma cutar ta kashe mutum 420 a Najeriya, wadanda 33 daga cikinsu sun rasu ne a kwanaki hudun da suka wuce.
Alkaluman ranar 15 ga watan Yuni sun nuna mutum 403 ne suka kamu da cutar a ranar daga jihohi 20.
Yanzu mutum 10,445 ne suka rage a Najeriya dauke da cutar coronavirus wadda aka riga aka yi wa mutum 92,924 gwajinta.
Bayanai daga hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya sun ce jihar Kuros Riba ce kadai cutar ba ta bulla ba kasar.