✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana 3 bayan kashe Limamin coci, matasa sun kone ofishin ’yan sanda a Neja

Matasan sun fusata tare sa kone ofishin 'yan sandan yankin.

Kwanaki uku bayan wani harin da aka kashe wani limamin cocin Katolika na St. Peter da ke Kafin-Koro, Karamar Hukumar Paikoro a Jihar Neja, rahotanni sun ce wasu fusatattun matasa sun kone wani ofishin ‘yan sanda a yankin.

Aminiya ta tattaro cewa lamarin ya faru ne lokacin da matasan suka taru da safiyar ranar Talata a gidan marigayin domin yi masa addu’a ta musamman gabanin a birne shi a ranar Alhamis.

Wasu majiyoyi sun ce mata da matasa mabiya addinin Kirista ne suka yi addu’a ta musamman kan wadanda suka kashe limamin cocin.

Har yanzu dai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ba ta bayar da sanarwa a hukumance game da kone ofishin ‘yan sandan ba.

Bugu da kari, kokarin wakilinmu samun Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Ogundele Ayodeji da Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ci tura.

Amma wani amintaccen jami’in rundunar ya tabbatar wa wakilinmu faruwar harin.

Ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya hada tawaga don kai ziyara ofishin da lamarin ya faru.

An ce rikicin ya samo asali ne lokacin da matasan suka bukaci kan dole sai ‘yan sandan da suka zo ba su kariya a wajen addu’ar sun tafi.

Lamarin dai ya haifar da rudani wanda ya kai ga kone ofishin ‘yan sandan yankin.