✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta sasanta ministocin da ke rikici da juna

Ministocin biyu daga yankin Kudu Maso Kudu dun dade suna zaman doya da manja

Shugaban Kwamitin Riko na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Bunin na Jihar Yobe, ya sulhunta rashin jituwar da ke tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva.

Amaechi wanda shi ne Ministan Sufuri yana takun saka da Ministan Albarkarun Man Fetur, Timipre Sylva saboda bambancin ra’ayi na siyasa.

Jiga-jigan ’yan siyasar biyu sun fito ne daga yankin Kudu maso Kudu kuma karkashin inuwar jam’iyya daya ta APC.

Ministocin biyu sun isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Litinin, inda suka yi ganawar sirri tare da Gwamna Buni da sauran kusoshin jam’iyyar da ta kai an sasanta tsakaninsu.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan ganarwar ta su ta sirri, Amaechi wanda ya fito kafada-da-kafada tare da Sylva, ya ce sun yanke shawarar su hada kai su yi aiki tare domin cimma manufofin jam’iyyarsu.

Haka zalika cikin sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa Yekini Nabena ya fitar, ya ca Gwamna Buni ya nemi ministocin biyu da su hada kai wuri guda domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben gwamna na jihohin Edo da Ondo da za a gudanar a watan gobe da na jibi.