Kwamitin Shugaban kasa Na Farfado da Yankin Arewa Maso Gabas (PCNI) ya kulla wata yarjejeniya da Cibiyar Da Ke Kula da Mulkin Dimokuradiyya da Samar da Ci Gaba (CDD) wajen hada gwiwa don a ci gaba da samar da zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana a yankin Arewa maso Gabas.
Dukkan kungiyoyin biyu sun kulla wannan yarjejeniya ce a ranar 22 ga watan Nuwamban wannan shekara a Abuja. Sun ce sun yi haka ne don ci gaba da bin hanyoyin da za a cigaba da samun wanzuwar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a yankin da yakin Boko Haram ya daidaita.
Shugaban kwamitin PCNI Latana-Janar T.Y. danjuma ya ce ana bukatar hada karfi da karfe wajen ganin an ci gaba da ceto yankin Arewa maso Gabas. Ya yi wannan bayani ne ta bakin Mataimakin Kwamitin Mista Tijjani Tumsah wanda ya wakilce shi a yayin kulla yarjejeniyar. Ya ce idan aka hada kai da kowane bangare za a samu damar ceto yankin daga bala’in da yake ciki da hakan zai kawo ci gaba ba a yankin kawai ba, har ma da daukacin Najeriya.
Mista Tumsah ya ce: “Hada kai ne ya fi dacewa don ganin an ceto yankin Arewa maso Gabas, da hakan zai kawo zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa”. Sannan wani muhimmin abu game da yin haka shi ne za a rika samun hadin kai wajen kawar da duk wata matsalar da za ta iya tasowa a yankin ta hanyar maganceta cikin gaggawa da kuma tabbatar da matsalar ba ta kawo nakasu a nasarorin zaman lafiya da na cigaba da aka riga aka samu a yankin ba. Ya tabo batun tsageranci da kuma na yi wa kowane bangare adalci. Ya ce hanyar da kwamitin shugaban kasa ya dauka na samar da dokar kare hakkin dan Adam a yankin abu ne da ya dace don hakan zai ba da damar share hawayen wanda aka zalunta da kuma samar da mafita ga wadanda yakin ya shafa.
Ya ce ya lura da yawa daga cikin ’yan gudun hijirar da ke zaune a sansanoni daban-daban (IDPs) suna son komawa garuruwansu na asali idan aka samar da zaman lafiya don ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.
A nata jawabin, Daraktar Cibiyar CDD, Misis Idayat Hassan ta ce akwai bukatar a hada karfi da karfe don ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da kuma bunkasa yankin Arewa maso Gabas. Ta ce Cibiyar CDD a shirye take wajen hada kai da kowace irin kungiya wajen ganin an samar da zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana a yankin Arewa Maso Gabas. Ta ce cibiyarta za ta yi aiki kafada da kafada da kungiyoyin sa kai na kasashen ketare da kuma na cikin gida don ganin an shawo kan matsalolin da ke addabar yankin Arewa maso Gabas.
Daga nan ta yaba da tayin da Kwamitin PCNI ya yi wa cibiyarsu na hada kai tare don a samar da ci gaba a yankin a kan haka ta bukaci sauran kungiyoyi da ke zaune a yankin Arewa maso Gabas da su hada kai da kwamitin PCNI wajen ganin an ceto yankin Arewa maso Gabas daga bala’in da ya auka.