✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin PCNI ya gana da wakilai da shugabannin al’umma a Jihar Yobe

A ranar 4 ga Disamban nan ne Ofishin Jihar Yobe na Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI), ya gana da wakilan…

A ranar 4 ga Disamban nan ne Ofishin Jihar Yobe na Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI), ya gana da wakilan Majalisar Dokokin Jihar Yobe da shugabannin kananan hukumomin Gujba da Gulani. Ganawar an kira ta ce domin wayar da kan mahalarta kan ayyukan Kwamitin PCNI a jihar. Gujba da Gulani suna daga cikin yankunan da hare-haren Boko Haram suka fi yi wa illa, inda suka hadu da barna da rushe-rushen gine-gine da hanyoyi da kadarorin jama’a da suka hada da gidaje da shaguna da gonaki da motocin da sauran kadarorin mutanen yankunan. Kuma sun hadu da gagarumar kaura sakamakon lalata muhallan mutane yankin. A baya-bayan nan Hukumar Kula da ’Yan gudun Hijira ta Duniya (IOM) da Gano Wadanda Aka Raba da Muhallinsu (DTM) ta ce, a yanzu fararen hula suna komawa wadancan yankuna bayan samun nasarar da sojoji suka yi. Kwararar masu komawa garurunwansu ya kara jawo wasu jerin matsaloli da suka hada da ta muhalli da abinci da kiwon lafiya da ruwan sha da kuma tsabta da sauransu.

Gwamnatin Jihar Yobe ta hannun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar suna hada hannu da kimanin hukumomi da kungiyoyin bayar da tallafin jin kai guda tara a sassa daban-daban domin tallafa wa wadanda suke dawowar. Ofishin Kwamitin PCNI na Jihar yana ci gaba da lura da kuma auna gibin da ake samu a wannan yunkuri. Taron ganawar wata kungiya mai zaman kanta ce mai suna boice and Accoutability da tallafin kungiyar PERL’s Engage Citizens Pillar (ECP), suka dauki nauyinsa domin tattaro masu ruwa-da-tsaki wurin daya su tattauna wasu batutuwa da suke tasowa a wadannan garuruwa da ake dawowa. Wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin kananan hukumomin biyu (Gujba da Gulani) da ’yan majalisa masu wakiltar yankin a Majalisar Dokokin Jihar da kuma mambobin kungiyoyin kare hakkin jama’a da ’yan jarida.

Ofishin PCNI na jihar ya gabatar da irin ayyukan da yake gudanrwa a jihar a daukaciin sasssa. Musamman a cikin gabatarwar akwai daukin da PCNI ya kai a sashen kiwon lafiya, inda ya bayar da kyautar magunguna da na’urori da motocin daukar marasa lafiya ga Ma’aikatar lafiya ta Jihar Yobe. Kuma an bayyana yadda PCNI ya yi kokarin yaki da cutar ciwon hanta ta ‘Hepatitis,’ inda ya dauki nauyin gwajin gano masu cutar tare da yin allurar rigakafi, kuma a kwanakin baya ya samar da na’urar duba masu fama da cutar, irinta na farko a daukacin yankin Arewa maso Gabas.

An sanar da taron kokarin da PCNI ya yi wajen nemo taimako daga kamfanoni masu zaman kansu domin farfado da yankin Arewa maso Gabas. A irin wannan kokari ne, Hukumar Fansho ta kasa (PENCOM) a kwanakin baya ta kai ziyara ga al’ummmomin biyu da ke jihar, inda ta nuna niyyarta ta gina ajujuwa goma a karkashin shirinta na kyautata rayuwar al’umma. Wakilan al’umma daga Gujba da Gulani sun roki PCNI ya gaggauta kammala ayyukan raya kasa a yankunansu, ta yadda za a gaggauta sake tsugunar da masu komowa gida. Ayarin Kwamitin na PCNI ya yi tambayoyi kan sassan da suke bukatar tallafi da yadda inda za a hada hannu.

Manajan Shirin PCNI na jihar ya bayyana kyakkyawar dangantakar da ke akwai a tsananin ofishin shirin na jihar da Gwamnatin Jihar Yobe.