Gwamnatin Jahar Adamawa ta sanya kwamitin bincike domin gano musabbabin fadan da ya faru a garin Numan, wanda a halin yanzu kwamitin ya samu rahotanni goma daga garuruwan da fadan ya shafa.
Shugaban kwamitin binciken, Mista Adamu Hobon ya bayyana haka ne ga manema labarai a Talatar da ta gabata.
Hobon ya bayyana cewa wadannan rahotonni da suka samu daga garuruwa goma a matsayin alama ta samun nasarar gano bakin zaren wannan binciken. Ya ce yadda garuruwan suka ba su hadin kai na tattaro rahotonnin, abin yabawa ne kuma alama ce ta kara masu kwarin gwiwa domin ci gaba da binciken, kamar yadda gwamnatin jihar Adamawa ta umurce su.
“A halin yanzu dai mun samu rahotonni goma daga garuruwan da fadan ya shafa, wadanda suke daga kananan hukumomin Numan da Demsa da kuma Lamurde,” inji shi.
Shugaban kwamitin, wanda tsohon alkali ne, ya ba da shawara ga sauran garuruwan da ba su riga sun tattaro nasu rahotonnin ba, da su yi hakan domin a san yadda za a magance matsalar a kan lokaci. Ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta kara ba su lokaci, domin sake samun rahotannin garuruwan da ba su riga sun mika tasu takardar ba.
Ya umurci sauran garukan da su hanzarta wajen mika na su takardar rohoto a lokaci.
An kafa wannan kwamitin bincike ne a 13 ga watan Disambar bara, wanda a yanzu ya rage masu makonni shida da su mika wa gwamnatin jiha cikakken rahoto game da ainihin matsalolin da ke haifar da wadannan fadace-fadacen.