✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum bakwai a Abuja

Mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya sakamakon barkewar annobar Kwalara.

Hukumomi a Babban Birnin Tarayyar Najeriya na Abuja, sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon barkewar annobar Kwalara.

Mukaddashin Sakataren Hukumar Lafiya a Abuja, Dokta Mohammed Kawu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, ya ce kawo yanzu an samu mutum 91 da suka kamu da cutar.

A cewarsa, mutanen da suka mutu bayan barkewar annobar sun fito ne daga yankin al’ummar Wassa da ke kwaryar birnin.

Sai da ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa a Gundudomin Bwari da Gwagwalada inda aka samu wadanda suka kamu da cutar.

Dokta Kawu ya umarci duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya da su fantsama wajen yin duk wata mai yiwuwa domin shawo kan wannan kazamar annobar kafin lamarin ya ta’azzara.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon nan ne hukumomi suka sanar da mutuwar mutum 119 da suka yi fama da cutar amai da gudawa a Jihar Kano.