✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 30, wasu 2,000 na asibiti

Cutar ta yi barna a kananan hukumomi tara na Jihar Jigawa.

Akalla mutum 30 sun rasu, wasu sama da 2,000 kuma na kwance a asibiti sakamakon barkewar cutar kwalara a Jihar Jigawa.

Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Salisu Mu’azu, ya ce galibin wadanda suka kamu da cutar a cikin wata biyu da suka gabata kananan yara ne.

Ya ce daga cikin kananan hukumomi tara da aka samu bullar cutar, abin ya fi tsanani a Hadejia, Dutse, Kirikasamma, Birnin Kudu da kuma Ringim.

Sai dai ya bayyana cewa an sallami wasu daga cikin mutum 2,000 da cutar ta kwantar a asibiti, ragogwar kuma suna ci gaba da samun kulawa a asibitocin gwamnati.

Duk da yake bai bayyana musabbabin barkewar cutar ba, Babban Sakataren ya alakanta na Karamar Hukumar Hadejia da amfani da gurbataccen ruwa.

Ya ce babu mamaki a samu gurbacewar ruwa a wuraren da mutane suke yin ba-haya a fili a kusa da wuraren da ’yan ga-ruwa ke samun ruwan da suke sayar wa jama’ar garin.

A cewarsa, gwamnatin jihar na kokarin shawo kan matsalar kuma tana kai daukin da ya dace ga mutanen yankunan da aka samu bullar cutar.

Ya ce Asusun kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya turo magunguna tare da alkawarin wasu nan ba da jimawa ba.