✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kusan duk mata na ajiye bidiyon tsiraicinsu a wayoyinsu — Safara’u

Ta ce kusan kaso 70 na mata na yin bidiyon su ajiye a wayarsu

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta shirin Kwana Casa’in, Safeeya Yusuf, wacce aka fi sani da Safara’u  ta ce kusan duk mata na ajiye bidiyon tsiraicinsu a wayoyinsu.

Safara’u, wacce ke tsokaci a kan wani bidiyonta na tsiraic da ya bayyana, ta ce daga cikin mutanen da take tare da su ne ya yada shi a shafukan sada zumunta.

Ta bayyana haka ne a wata tattaunawarta da Sashen Hausa na BBC a ranar Talata.

Jarumar wadda idan ba a manta ba, ta daina fitowa a shirin na Kwana Casa’in bayan bidiyon tsiraicinta ya bayyana a kafofin sadarwa, ta ce tana yin bidiyon tsiraicinta ta ajiye domin nishadi wanda kuma kashi 70 cikin 100 na mata na yi su a ajiye a cikin wayoyinsu.

“[Bidiyon tsiraicina-]bidiyo ne wanda ni ina yi in ajiye a wayata [don nishadi ko wani abu mai kama da haka]. Kuma wanda ni na san [kusan] a cikin kaso 100, kaso 70 na mata suna wannan abin su ajiye a wayarsu…,” a cewarta.

Har wa yau, ta ce wani ne ko wata daga cikin makusantanta ya yada bidiyon saboda ita dama tana da dabi’ar yin bidiyon tsiraicinta ta ajiye a wayarta.

“Bazance kai tsaye ga wanda ya dauki bidiyon ya fita da shi ba amma dai nasan cewa lallai cikin wadanda nake tare da su ne, saboda ina yawan ba da wayata ga kawayena ko wadanda muke tare da su…”

Idan ba ku banta ba a baya lokacin da bidiyon nata ya fita, jarumar ta shaida wa cewa ta shiga damuwa sosai.

Safara’u ta ce, “Na shiga damuwa sosai, amma ban nuna wa kowa ba, kuma ban ce komai ba. Abin da ya zo min zuciya shi ne, akwai alamar zan samu daukaka a gaba shi ne hakan ya faru.”

Har wa yau a sabuwar tattaunawar ta ce sai da ta yi wata uku ba ta fita ba bayan fitar bidiyon tsiraicin nata saboda kunyar jama’a.

Dangane da yadda take waka da maza  da ma sauran harkokinta, jarumar ta ce rashin samun abokiya mace da za su rika harka tare ne ya sa take yi da maza kuma yin wakar da su ya fi sa wakokin nata su karbu.

“Har yanzu ban samu mace guda daya da zamu yi waka da ita ba, kuma dama 442 mutumina ne tun da dadewa”