✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar kwadago ta yi watsi da karin kudin mai

Kungiyar ta ce karin ba abu ne da za ta lamunta ba

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi fatali da matakin Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) na yin karin kudin man fetur.

Shugaban kungiyar na Najeriya, Kwamared Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, lokacin da yake jawabi ga ’yan jarida.

Rahotanni sun bayyana cewa gidajen mai mallakin NNPC dai sun mayar da farashinsu sama da Naira 500 a galibin sassan Najeriya.

Matakin dai na zuwa ne kwana biyu bayan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da janye bayar da tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki a ranar Litinin.

To sai dai Shugaban na NLC ya bayyana karin kudin a matsayin rashin tausayi, inda ya ce sam ba za su lamunci duk wata tattaunawa ba a kai a nan gaba, matukar ba a janye shi ba.

Ya ce ’yan kwadagon ba za su lamunci matakin gwamnati na janye hannunta daga harkar mai ba, amma kuma ta ci gaba da kayyade farashinsa.

“Mun damu matuka da yadda duk da tattaunawar da masu ruwa da tsaki suka sha yi a kan nuna rashin amincewa da matakin Shugaba Tinubu, amma sai NNPC yau da safe ya yi gaban kansa ya kara farashin.

“Wannan ba daidai ba ne, kuma ya saba da matakin tattaunawa da samun daidaito, wacce ita ce hanya mafi a’ala ta kawo karshen kalubalen man fetur,” in ji shi.

Daga nan sai Shugaban na NLC ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya gaggauta umartar NNPC ya janye abin da ya kira “farashin rashin kan gado” domin a samu damar ci gaba da tattaunawa.