✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya kamata a soke hukumomin zaben jihohi’

Wata kungiya ta ce ya kamata INEC ta karbe ragamar gudanar da zaben kananan hukumomi.

Wata kungiya mai zaman kanta da ke rajin ci gaban Najeriya, Pro-Nigeria Group (PNG), ta yi kiran da a soke dukkanin hukumomin zaben jihohin kasar nan.

A cewar kungiyar wacce ba ta da alaka da harkar siyasa, hukumomin zaben sun zama kafofin da gwamnonin jihohin ke amfani da su wajen karya lagon kananan kukumomin kasar.

Wannan kira ya fito ne daga Babban Daraktan Gudarnarwar kungiyar, kuma Shugaban rukunin Kamfanonin CFL, Lai Omotola.

A yayin wani taro da kungiyar ta gudanar a yankin Maryland na birnin Ikko a Jihar Legas, Omotola ya shawaraci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), da ta karbe ragamar gudanar da zabuka daga matakin Kansila har zuwa Shugaban Kasa.

“Idan ba mu kwato ’yancin Kananan Hukumominmu ba, to hakika kuwa ba za mu taba samun cikakken mulkin dimokuradiyya ba a kasar nan,” inji shi.

Kazalika, Omotola ya koka kan yadda masu fafutikar neman ballewa da wasu kungiyoyin ’yan aware ke yi, inda ya ce yanzu bukatar neman a yi daunin iko tare da bai wa mutane a matakin Kananan Hukumomin iko shi ne abu mafi a’ala ba tayar da jijiyar wuya a kai.