✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudurin dokar hana yanka jakuna ya tsallake karatu na biyu

Kudirin dai na neman Najeriya ta amfana da kasuwar fatar jakunan wacce ake fitarwa kasashen ketare.

Wani kuduri da ke neman a ayyana dokar da za ta haramta yanka jakuna babu kaidi a Najeriya ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Dattijai ranar Talata.

Dan majalisa na jam’iyyar APC daga Jihar Kebbi Sanata Yahaya Abdullahi ne ya gabatar da kudurin tun da farko.

A cewar Sanata Yahaya, wanda kuma shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, babbar bukatar kudurin ita ce bai wa Najeriya damar amfana da kasuwar fatar jakin wacce ake fitarwa kasashen ketare a sarrafa.

“Muna bukatar gwamnati ta rika kula da harkar ne ba wai ta hana ba baki daya ta yadda za a durkusar da masu yinta su koma fita da fatar ta barauniyar hanya saboda tsananin bukatar da ake mata musamman a kasar China.

“Dokar za kuma ta samar da damar da jakunan za su rika hayayyafa ta yadda masu sha’awar kiwonsu don kasuwanci za su iya yin haka ta hanyar bin sharuddan da za a gindaya musu,” inji shi.

Sanata Yahaya ya kara da cewa an yi wa kudirin karatun farko ne tun ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2020.

Taken kudurin shi ne: “Bukatar a kafa dokar da za ta hana ci gaba da yanka jakuna ta kuma kafa wuraren kiwo tare da killace su da kuma kauce wa gushewarsu baki daya ta 2021”.

Hurumin majalisa

Sai dai ana tsaka da tafka muhawara a kan kudurin ne sai Sanata Eyinnaya Abaribe na PDP daga Jihar Abiya ya ce yin doka a kan batun ba ya cikin hurumin majalisar.

Amma da yake mayar masa da martani, Sanata Yahaya Abdullahi ya ce, “Ni kwararren likitan dabbobi ne, kuma zan iya tuna lokacin da a Ma’aikatar Aikin Gona aka tattauna batun barazanar karewar jakuna sannan aka amince da shi yayin taron Hukumar Aikin Gona da Raya Karkara ta Ƙasa a Jihar Sakkwato a shekarar 2004.

“Wannan kudurin wani abu ne da kasar nan ke bukata kuma ya kamata mu goya masa baya”.

A baya-bayan nan dai ana nuna damuwa game da yadda ake yanka jakuna ba tare da lissafi ba don fitar da fatunsu zuwa waje, lamarin da ya haifar da faragabar karewarsu.

Ko a shekarun baya ma, Majalisar Wakilai ta amince da kudurin dokar da za ta haramta yankawa da fitar da fatun jakuna zuwa kasashen ketare.