Darakta Janar na Hukumar Kula da Kare Ruwan Najeriya (NIMASA) Dokta Dakuku Peterside ya ce nan ba da jimawa ba Majalisar Dokoki ta kasa za ta amince da kudirin dokar yaki da masu yi wa jiragen ruwa fashi da makami a cikin teku.
Shugaban ya bayyana cewa kudirin dokar an tsara shi ne yadda zai magance miyagun ayyukan da ake tafkawa a ruwan Najeriya.
A kwanakin baya kasar Amurka ta hannun Hukumar Kula da Ruwanta ta fitar da wani rahoto da ke gargadi ga jiragen ruwan dakon kaya kan su rika yin taka-tsantsan duk lokacin da suka tunkaro tekun Najeriya.
Da yake jawabi ga manyan shugabannin Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), wadanda ya kai musu ziyarar girmamawa, Mista Peterside ya ce, “An kammala komai a yanzu” domin a amince da dokar yaki fashi a cikin teku.
Da Shugaban na NIMASA ke tattauna batun mai kanun, “Gabatar da Shudin Tattalin Arziki” ya ce kudirin dokar wanda aka tsara shi a matsayin kudirin bangaren zartarwa dauke da dabaru, Shugaban kasa ne zai gabatar ga Majalisar Dokoki ta kasa domin ba ta karfi da gaggawar da take bukata.
Ya ce dokar tana da muhimmanci, saboda Najeriya ba ta da dokokin yaki da fashi a cikin teku, inda ya mafasan cikin teku da ake kamawa, ana yi musu hukunci ne da dokokin da ba su da alaka da fashi a cikin teku.
“Ana sa ran a watan gobe za a amince da kudirin dokar a Majalisar Zartarwa ta kasa daga nan sai a mika ga Majalisar Dokoki ta kasa. Ina da yakinin nan da zuwa shekara mai zuwa za mu samu wannan doka,” inji shi.
Ya ce yana da yakinin Najeriya za ta iya samun Dala miliyan 40 daga albarkatun da suke cikin teku, inda aka yi kyakkyawan tsari.
Sai ya bugi kirjin cewa, a yayin da Najeriya har yanzu take dogara da albarkatun kasa, ya ce, kasar nan za ta samu albarkatu masu dimbin yawa a cikin teku da za su bunkasa tattalin arziki.
A jawabin, Shugaban Hukumar NSC, Barista Hassan Bello ya ce akwai bukatar su hada karfi da Hukumar NIMASA wajen samar da tsarin da zai sa a samu bunkasa a bangaren sufurin jiragen ruwa a kasar nan. “Muna kira ga NIMASA ta taimaka mana wajen magance wasu batutuwa da muke da su, kuma ta tabbatar da cewa ana bin wasu tanade-tanaden da aka tsara,” inji Bello.