✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku sa ido sosai kan baki masu shigowa – Sarkin Fika

Sarkin ya yi kiran ne a sakonsa na barka da Sallah.

Mai Martaba Sarkin Fika da ke Jihar Yobe, Alhaji Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu IIdriss, ya yi Kira ga al’ummar masarautar da Jihar da su sa ido da kai rahoton bakin da ba su yarda da take-taken su ba.

Sarkin, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Sarakuna Jihar Yobe ya yi kiran ne ranar Talata a sakon sa na Babbar Sallah ga jama’ar Jihar.

Ya kuma yi Kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen yaki da masu garkuwa da mutane da suka addabi kasar nan.

Gami da tsadar abincin da ake fama kuwa, ya roki gwamnatocin Jihohi da ta tarayya da su samar da tallafi ga jama’a don samun saukin rayuwa.

Sarkin ya kuma godewa matasa da samari kan aikin gayya da suke yi na share magudanun ruwa da gyaran makabartu a cikin gari.

A gefe guda kuma, ya yi kira ga iyayen da  su fara gudanar da allurar rigakafin Zazzabin Cizon Sauro na yara ’yan watanni uku zuwa shekara biyar.

Daga karshe yi kira ga wadanda ba su yi rijistar zabe ba da su tabbatar duk wanda ya kai shekara 18 ya je ya yi.