✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku ji tsoron mummunan karshe (1)

Daga hudubar Sheikh Abdul’aziz bin Abdullahi Alu Assheikh Masallacin Imam Turki bin Abdullahi Fassarar Salihu Makera Hamdala da mukaddima: Bayan haka, ya ku mutane, ku…

Daga hudubar Sheikh Abdul’aziz bin Abdullahi Alu Assheikh

Masallacin Imam Turki bin Abdullahi

Fassarar Salihu Makera

Hamdala da mukaddima:

Bayan haka, ya ku mutane, ku ji tsoron Allah hakikanin jin tsoronsa. Bayin Allah! Allah Madaukaki Wanda Shi ne Mafi gaskiyar masu magana Yana cewa: “Kuma ka ce, ku yi aiki, sa’annan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin fake da bayyane, sa’annan Ya ba ku labari kan abin da kuka kasance kuna aikatawa.” (9: 105)

Dan uwa Musulmi! Mu yi tadabburin wannan aya, Allah Ya umarce mu da yin aiki, ba a hallice mu don wasa ba, an hallicce mu ne don mu bauta wa Allah, an hallicce mu ne domin mu rika aiwatar da umarnin Allah, an hallicce mu ne, domin mu sauke abin da Allah Ya wajabta mana, mu bauta maSa da wannan shari’a, mu tsayu wajen tabbatar da hakikaninta a ilimance da aikace a fili da boye, domin mu kasance muminai na gaskiya. “Ka ce ku yi aiki sa’annan Allah zai ga aikinku da ManzonSa.” Allah Ya riga Ya san abin da bayi suke aikatawa, amma Madaukaki ba Ya yin ukuba ga bawa har sai sabonsa ya bayyana an kafa hujja a kansa. “Da sannu Allah zai ga aikinku da ManzonSa da Muminai, sannan a mayar da ku zuwa ga Masanin fake da bayyane, sannan Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa.”

Lallai makomarku zuwa ga Masanin fake da bayyane take, iliminSa ya daidaita wajen sanin abin da yake boye da abin da yake fili; “Ka ce idan kun boye abin da ke a cikin kirazanku ko kuwa kun bayyana shi, Allah Yana saninsa, kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da kasa, kuma Allah a kan komai Mai ikon yi ne.” (K:3:29).

Ya kai Musulmi! Aikinka ba zai zamo aikin kwarai ba, har sai ya kasance ya dace da niyyar kwarai a zuciya da furuci, a harshe da kuma aikata shi da gabbai. Aiki na zahiri a lokacin da zuciya ta wofinta daga i’itikadi da yakini ba zai yi amfani ba, sannan i’itikadin da aiki na zahiri bai fassara shi ba, ba zai amfanar ba, don haka ba makawa ya zamo zahiri da badini su daidaita. A badini a samu tsarkake aiki don Allah da tsayuwa wajen sauke abin da Allah Ya dora wa bawa, zuciya ta bauta wa Allah cikin kankan da kai da rashin jiji da kai, a zahiri kuma a tsayu da abubuwan da aka wajabta tare da barin abubuwan da aka haramta, haka aiki mai amfani yake, haka aiki mai amfanarwa yake, kuma haka ya wajaba mumini ya kasance a rayuwarsa, ya tafiyar da rayuwarsa cikin alheri yana mai bauta wa Allah da dukkan gabbansa a zahiri da badini.

Ya kai Musulmi! Ka sani abin da ake jin tsoro ga mutum shi ne ya bayyana alheri a fili ya boye akasinsa, ko ya bayyana riko da addini da hali nagari, alhali a zuciyarsa sabanin haka ne, ayyukansa na fili lullube da riya da son a ji. Ba don Allah yake Sallah ba, ba don Allah yake aikin da’a ba, ba don Allah yake layya ba, ba don Allah yake ibada ba. Wadannan al’amura suna yaudarar da ma’abucinsu, don haka ne magabatan kwarai na wannan al’umma suke ji wa kansu tsoro, suna jin tsoron kada ayyukansu su yaudarar da su, sai suka hada tsakanin tsoron Allah da kyautata aiki. “Lallai ne wadanda suke masu sauna saboda tsoron Ubangijinsu. Da wadanda suke game da ayoyin Ubangijinsu suna imani. Da wadanda suke game da Ubanginjinsu ba su yin shirki. Da wadanda ke bayar da abin da suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsorace domin suna komawa zuwa ga Ubangijinsu.” (K:23:57-60).

Wadannan mutanen kwarai, suna tsoron kada riya ta bijiro wa ayyukansu ta bata ayyukan, ko kuma-abin Allah Ya kiyaye-shakku da kai-kawo su shafi ayyukan, su bata su. Suna tsoron ayyukansu ba su dogara da ayyukan da suke yi, sun fi neman mafaka zuwa ga Allah, sun fi karfafa kwadayi cikin nuna tsananin bukata a wurin Ubangijinsu, su a kullum cewa suke: “Ya Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukatanmu bayan Ka shiryar da mu, kuma Ka ba mu rahama daga wurinKa. Lallai ne Kai, Mai yawan kyauta ne.” (K:3:8). Kuma suna tunawa da fadin Allah ga AnnabinSa: “Kuma ba domin Mun tabbatar da kai ba, lallai ne, hakika da ka yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kadan. A lokacin, lallai ne da Mun dandana maka ninkin azabar rayuwa da ninkin azabar mutuwa, sa’annan kuma ba za ka samu mataimaki ba a kanMu.” (K: Isra’i: 74-75).

Lallai mumini yana aiki, sai dai yana sanya idonsa kan yadda karshen al’amarinsa zai kasance, ba ya sanin da me rayuwarsa za ta cika. Yana tsoron kada ya juya daga imani zuwa ga kafirci, ko daga mikakkiyar hanya zuwa ga karkata, ko daga lizimtar tafarkin kwarai zuwa ga nesantarsa. Yana lura da yadda mutane suke bin son zukatansu, kwakwalesu suna canjawa, ra’ayoyinsu suna nan nau’i-nau’i, yau suna masu kira zuwa ga alheri da kyautatawa, gobe kuma suna rusa ginin da suka yi, suna caccanja abin da suka ce da miyagun ayyuka. Don haka mumini yana tsoron abin da zai faru da ransa, kan kada Shaidan ya rinjaye shi ya mantar da shi ambaton Allah, kuma ya kange shi daga tafarkin Allah madaidaici, yana tsoron kada Shaidan ya sanya masa rufi a kan zuciyarsa da miyagun ayyuka, ya je ya sadu da Allah ba yana shiryayye ba, Allah Ya yi mana tsari daga haka baki dayanmu. Don haka ne Allah Ya ce wa bayinSa, “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (Musulmi).” (K:3:102). Don haka ku lizimci Musulunci, ku tabbata a kansa, ku tsayu a kansa har mutuwa ta zo muku kuna masu lizimtar Musulunci, ba masu canjawa ko jirkita addini ba.

Ku saurari abin da Allah Ya fada kan AnnabinSa Ya’akub: “Kuma Ibrahim ya yi wasiyya da ita ga ’ya’yansa, kuma Ya’akubu (ya yi wasiyya, suka ce:) “Ya ’ya’yana! Lallai Allah Ya zaba muku addini, don haka kada ku mutu, lallai, face kuna Musulmi.” (K:2:132). Ku lizimci Musulunci a ilimance da aikace, ku rayu kansa a zahiri da badini, ku roki Allah tabbata a kan gaskiya, domin lallai zukatan bayi a hannun Allah suke, Yana jujjuya su yadda Ya so. Kuma Shugaban ’ya’yan Adam, Shugaban na farko da na karshe, jagoran Annabawa da Manzanni a kullum yana addu’a yana cewa: “Ya Ubangiji! Mai jujjuya zukata, Ka tabbatar da zuciyata a kan addininKa.” Sai A’isha ta tambaye shi shin kana jin tsoro ne Ya Manzon Allah? Sai ya amsa mata da cewa: “Lallai zukatan bayi suna tsakanin yatsu biyu na yatsun Mai rahama, Yana jujjuya su yadda Ya so, idan Ya yi nufin juya zuciyar wani bawa sai Ya juya ta.”

Ya kai Musulmi! Yana daga cikin alamar dacewa da yardar Allah a gare ka da alamar cikawa da alheri a gare ka, a ce ka dace a abin da ya saura na karshen rayuwarka ta wajen aikata ayyuka na kwarai, ka daidaita a kansu ka tabbata a kansu, sauran rayuwarka ta rika gudana a kansu. Anas (RA) yana cewa: Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan Allah Ya nufi bawa da alheri sai Ya ba shi aiki.” Sai suka ce: “Yaya zai ba shi aiki Ya Manzon Allah?” Sai ya ce, “Ya datar da shi ga aikata aikin kwarai, kafin ya mutu.” Wato Allah zai sa ya riski tuba ta gaskiya, ya musanya munana ayyukansa da kyawawa, ya ciru daga zaluntar bayi, ya tuba zuwa ga Allah daga miyagun maganganu da ayyuka, har ya zamanto mutuwa ta zo masa, ruhi yana kokarin barin jikinsa a lokacin da shi kuma yake tabbace a kan gaskiya, yake tabbace a kan shiriya, har bushara ta zo masa yana gadon mutuwarsa: “Lallai wadannan da suka ce, “Ubangijinmu, Shi ne Allah,” sa’annan suka daidaitu, Mala’iku na sassauka a kansu (a lokacin saukar ajalinsu suna ce musu), “Kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi bakin ciki, kuma ku yi bushara da Aljanna wadda kun kasance ana yi muku wa’adi da ita. “Mu ne majibintanku a cikin rayuwar duniya da kuma a cikin Lahira, kuma a cikinta kuna da abin da rayukanku ke sha’awa, kuma kuna da abin da kuke kira (a kawo muku) a cikinta. A kan liyafa daga Mai gafara, Mai jinkai.” (41:30-32). Haka al’amarin zai kasance ga waliyan Allah masu gaskiya, wadanda suka tsarkake ayyukansu domin Allah, suka gaskata Allah cikin mu’amalarsu, ba su yin aiki don riya ko don a ji, ko don neman suna ko don neman daukaka a duniya ba. “Wancan gidan Lahira Muna sanya shi ga wadanda suke ba su nufin daukaka a cikin rayuwar duniya, kuma ba su son barna. Kuma akiba (kyakkyawar karshe) ga masu takawa take.” (K:28:83).

Ya kai Musulmi! Ka sani wajibi ne a kan Musulmi a koyaushe ya rika rokon Allah kyakkyawar karshe, ya roki Allah Ya sa karshen rayuwarsa ya cika da alheri, Ya sa abin da ya saura a rayuwarsa ya zama mafi alheri daga abin da ya gabata, a kullum ya rika cewa: “Ya Ubangiji! Ka sanya mafi alherin rayuwarmu ya zamo karshenta, kuma mafi alherin ranarmu ranar da za mu sadu da Kai a cikinta.”

Ya kai Musulmi! Neman kyakkyawar cikawa ce ke hana salihan bayi jin dadin kwanciya, kuma ta sa su kasa jin dadin rayuwar duniya. Ba wai mummunan zato suke yi ga Ubangijin talikai ba, Allah Ya tsare su daga haka, a’a tsananin tsoron kansu ne, kada a bijiro musu da munanan ayyukan da suka aiwatar da sabon da suka yi, suna tsoron kada su kasa neman tuba ko a ki karbar tubarsu, suna tsoron kada sha’awoyinsu su dauke su ga neman jin dadin duniya, rayuwarsu ta kare ba tare da wata fa’ida ba.Suna  ji wa kansu tsoro, suna aiki da fadin Allah Madaukaki: “Kuma abin da ya same ku na wata masifa, to game da abin da hannayenku suka sana’anta ne, kuma (Allah) Yana yafewar (wasu laifuffuka) masu yawa.” (K:42:30) Kuma “Lallai Allah ba Ya zaluntar mutane da komai, amma mutanen ne ke zaluntar kansu.” (K:10: 44).

Don haka ka roki Allah cikawa da alheri, ka roki Allah ka hadu da Shi kana Musulmi ba ka canja ba, ba ka jirkita ba, a’a kana tsaye a kan tafarkin shiriya.

Ya kai Musulmi! Sabubban cikawa da kyau suna da yawa, amma babbansu shi ne:

Jin tsoron Allah a boye da bayyane: “Ka ji tsoron Allah a duk inda ka kasance.” Kuma “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da takawa, lallai Allah Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa.” (K:59:18).

Takawa ta hakika: “To, lallai ne masoya (waliyan) Allah babu tsoro a kansu, kuma ba za su kasance suna yin bakin ciki ba. (Su ne) Wadanda suka yi imani, kuma suka kasance suna yin takawa.” (K:10:62-63). “Kuma wanda ya bi Allah da takawa, Allah zai sanya masa mafita.” (K:65:2).