✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta kori karar PDP kan zaben Osun

Kotun ta ce PDP ba ta hurumin jin ba'asin dawowl da Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kotun Koli ta kori karar da Jam’iyyar PDP ta daukaka na neman soke takarar tsohon Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola da mataimakinsa Benedict Alabi a zaben ranar 16 ga watan Yuli, 2022.

Wani kwamitin mutum biyar na Kotun Koli, karkashin jagorancin Mai Shari’a Centus Nweze a ranar Alhamis ya bayyana cewa karar da PDP ta shigar ba shi da wani tushe, inda ta umarci lauyan PDP Kehinde Ogunwumiju da ya janye karar.

Kotun ta ce PDP ba ta da hurumin bin ba’asin hukuncin dawo da takarar Oyetola da Alabi’ a APC a matsayin wanda suka lashe zaben fidd-da gwani.

Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yanke hukunci a ranar 30 ga Satumba, 2022, inda ya soke Oyetola da Alabi a matsayin ’yan takara a zaben gwamna bisa hujjar cewa mukaddashin shugaban Jam’iyyar APC na kasa a wancan lokacin Mai Mala Buni ne ya zabe su don yin takara.

Amma kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin a wani hukunci da ta yanke a watan Disambar bara, hukuncin da PDP ta daukaka zuwa Kotun Koli.

Idan ba a manta ba wata babbar kotun jihar ta soke nasarar Ademola Adeleke a zaben gwamnan jihar, bayan INEC ta rantsar da shi.