✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi wa matashi bulala 5 kan satar dabino a Kano

An same shi da laifin satar dabino kwano hudu.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano, ta bayar da umarnin yi wa wani matashi mai suna Alkasim Murtala bulala biyar bisa laifin satar dabino kwano hudu.

Murtala mai shekaru 25 wanda ke zaune a unguwar Koki a Kano, an same shi da laifuka biyu da suka hada da keta haddi da kuma aikata sata.

Alkalin kotun, Malam Isma’il Muhammad Ahmed, ya yanke wa wanda ake kara hukuncin zaman gidan yari na wata daya ko biyan tarar Naira 5,000 tare da bulala biyar, bayan ya amsa laifinsa.

Tun da farko, lauyan masu kara, Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wani Ahmed Malamai ne ya kai karar ofishin ‘yan sanda na Fagge da ke Kano a ranar 24 ga Janairu.

Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa cikin shagon Malamai da ke Kasuwar Sabon Gari, inda ya saci dabino kwano hudu wanda kudinsa ya kai Naira 10,000.

Wada, ya ce laifin ya ci karo da sashe na 133 da 120 na Kundin Laifukan Shari’a na Jihar Kano.