✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa wanda ya kashe abokinsa hukuncin rataya

Ya buge abokinsa Adamu Ibrahim da sanda a kai ne kafin ya yanke kan.

Ahmed Mohammed, Bauchi Babbar Kotun Jihar Bauchi Mai lamba 10 a karkashin Mai shari’a Faruk Umar Sarki, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai suna Musa Hamza da ta samu da laifin kashe abokinsa tare da kwakule idonsa kuma ya binne kai da gangar jikinsa a wurare daban-daban.

Kotun ta samu wanda ta yanke wa hukuncin da laifin kashe abokinsa, mai shekara 17 mai suna Adamu Ibrahim kuma ya yanke kansa, tare da kwakule idonsa da dandake kwayar idon, sannan ya binne kai da gangar jikinsa a wurare daban-daban bayan gabatar da kwararan shaidu a gaban kotun.

Tun farko lauyoyin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Bauchi, Mohammed Y. Ibrahim da Salihu A. Haruna da Ali S. Yusuf ne suka gabatar da karar inda suka tuhume shi da aikata kisan kai, wanda hukuncinsa kisa ne kamar yadda yake a karkashin Doka ta 221 bayan korafin da mahaifin matashin da aka kashe ya kai ga kotun.

Masu gabatar da karar sun shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya buge abokinsa Adamu Ibrahim da sanda a kai ne kafin ya yanke kan.

Lokacin da aka shaida wanda ake tuhuma zargin da ake yi masa ya musanta kafin shaidu su tabbatar da tuhumar da ake yi masa.

Mahaifin marigayin ya kai koken cewa dansa bai dawo gida bayan kiran da aka yi masa a waya kuma ya ce bayan kiran da abokin ya yi masa an samu labarin an ga matashin tare da wanda ake tuhuma sun fita su uku da dare inda suka ci abinci tare, daga baya daya abokin ya tafi ya bar su a wurin.

Bayan gudanar da bincike angano wayar mamacin a wurin wanda ake tuhumar, wanda haka ya sa aka ci gaba da bincike har ya amsa laifinsa. Ya ce shi ne ya ja mamacin zuwa daji ya kashe shi ya yanke kansa ya binne kan daban gangar jikin daban bayan ya cire masa idanu.

Ya shaida wa ’yan sanda cewa ya dandake idon ya sa a cikin kwalba a kan zai kai wa wani boka.

’Yan sanda sun tasa keyar wanda ake tuhuma ya nuna inda ya binne mamacin aka tono kan da gangar jikin a wuraren da ya binne aka kai asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Umar Faruk Sarki ya ce, bayanan da aka gabatar a gabansa sun tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata wannan laifi kuma kotu ta yanke masa hukuncin kisan kai, inda ya ki amincewa da rokon da lauyan wanda ake tuhuma na a yi masa sassauci.

Ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda yake a karkashin Doka ta 273 da ta 221 na Kundin Manyan Laifuffuka na Jihar.