✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare masu kwacen waya cikin shigar mata a Kano

Daya daga cikin mutanen ya shiga hannu ne a yayin da yake sanye da hijabi yana kokarin yin kwacen waya.

Kotun Majistare ta jihar Kano ta tsare wasu maza biyu da aka kama sun yi shigar mata suna yi wa jama’a kwacen waya da kuma fashi da makami.

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa daya daga cikin mutanen ya shiga hannu ne a yayin da yake sanye da hijabi yana kokarin yin kwacen waya.

Asirinsu ya tonu ne bayan sun yi shigar mata suka kwace wa wani mutum waya da babur dinsa da jimillar kimarsu ta kai Naira dubu 585 da 700.

Bayan sauraron bayanin ’yan sanda, alkalin kotun, Rabi Abdulkadir ta sa a ci gaba da tsare su.

Ta kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Mayu da muke ciki.