✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare masu gadi 2 a kurkuku kan satar katifun makaranta

Masu gadin sun amsa laifi ba tare da wahalar da kotu ba.

Wata kotun Abuja mai zamanta a yankin Karu, ta ba da umarnin tsare wasu masu gadi su biyu a gidan yari kan zargin satar katifun makaranta guda 69.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Umar Mayana, wanda ya ba da umarnin hakan ranar Laraba, ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Disamba.

Tun farko, lauya mai gabatar da kara, Olarewaju Osho, ya shaida wa kotun cewa mai karar wanda babban jami’i ne a wata makarantar Abuja, ya kai rahoton batun ofishin ‘yan sanda da ke Kurudu.

Mai tuhumar ya ce masu kare kansu sun saci babban talabijin inci 32 da katifun makaranta guda 69 wanda a kiyasce kudin kayan ya kai Naira miliyan uku da dubu dari daya.

“Yayin binciken ‘yan sanda, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu,” in ji Osho.

Haka nan, ya ce, laifin da suka aikata ya saba da sassa na 97 da 289 na kundin Penal Code.

(NAN)