✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sa ranar sauraron martanin da ake yi wa tuhumar Abduljabbar

Lauya ya ce tuhumar da ake yi wa malamin ba ta bisa ka'ida.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta sanya 19 ga Yulin 2022, a matsayin ranar fara sauraron martanin Lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano game da shari’ar da ake yi wa Abduljabbar Kabara.

An dai shigar da karar ce a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke jihar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Abdullahi Liman.

Tunda farko Lauyan Abduljabbar Kabara, watau Barista Dalhatu Shehu Usman ne ya garzaya gaban Babbar Kotun Tarayyar yana kalubalantar tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda yake karewa.

Lauyan ya ce tuhumar da ake yi wa malamin ba ta bisa ka’ida.

Sai dai Lauyan Gwamnatin, Barista Muhammad Dahuru ya shaida wa kotun cewa har zuwa wannan rana Lauyan Abduljabbar din bai ba su odar ba, hakan ya janyo ba su yi martani a kai ba.

A cewar Barista Dalhatu, a shirye suke su yi martani da zarar sun samu wannan oda a hannnunsu.

Idan za a iya tunawa, tun a watan Yulin shekarar 2021, Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotun bisa zargin yin batanci ga Annabi (S.A.W) da tayar da hankulan jama’a.