✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta raba auren dan kasuwa saboda raina suruki

Wata kotun Musulunci ta kashe auren wani dan kasuwa saboda cin zarafin da yake wa matarsa da kuma rashin girmama mahaifanta. Kotun da ke Magajin…

Wata kotun Musulunci ta kashe auren wani dan kasuwa saboda cin zarafin da yake wa matarsa da kuma rashin girmama mahaifanta.

Kotun da ke Magajin Gari, Kaduna, ta raba auren ne bayan matar dan kasuwan ta bukaci hakan saboda cin zarafi da kuma raina iyayenta.

Matar ta kuma bukaci kotun ta umarce shi ya rika ba ta N5,000 kan kowanne daga cikin ‘ya’ya takwas da suka haifa a matsayin kudin kulawa.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Murtala Nasir, ya umarci mijin kada ya kuskura ya sake shiga gidan da suke zama tare da matar a lokacin da suke a matsayin mata da miji.

Kotun ta kuma ba wa matar izinin amfani da sadakin N10,000 da mijin ya ba ta wurin ciyar da ‘ya’yan nasu har zuwa karshen watan Maris.

Alkalin ya bukaci kowanne daga bangarorin biyu ya da ke bukatar ci gaba da rike ‘ya’yan nasu da ya bi tsarin shari’a wajen yin hakan.

Kafin a kai ga raba auren, a baya kotun ta bukaci ma’auratan da su je su sulhunta, su warware matsalolin nasu cikin ruwan sanyi amma abin ya gagara.