✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta gayyaci Rarara kan zargin boye matar aure

Ana zargin mawakin da boye matar auren na tsawon watanni uku ba tare da sanin mijinta ba.

Wata babbar kotun Shari’ar Musulunci dake zamanta a Kofar Kudu cikin birnin Kano ta gayyaci fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara da ya bayyana gabanta.

Kotun dai ta bukace shi da ya gurfana a gabanta ranar 22 ga watan Disamban 2020 bisa zargin boye wata matar aure tare da saka ta cikin wani bidiyon wakar siyasa da ya yi.

Tun da farko dai mijin matar mai suna Abdulkadir Inuwa ne ya shigar da karar gaban kotun, inda yake zargin Rararan da saka matarsa wadda suke da aure a cikin bidiyon wakarsa mai suna ‘Jihata, Jihata ce‘.

Maigidan nata ya bayyana cewa tsawon watanni 3 kenan ba a san inda matar tasa ta shiga ba, don haka ya roki kotun da ta bi masa hakkinsa.

Alkalin Kotun mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya sanya ranar 22 ga Disamba don ci gaba da sauraron shari’ar kuma ya ba da sammaci ga Rarara don bayyana a gaban kotun.