✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure basaraken da ya yi garkuwa da kansa shekara 15

Wata babbar kotu a jihar Legas da ke zamanta a Ikeja, ta yanke wa Sarkin Shangisha da ke yankin Karamar Hukumar Alimosho a jihar, Michael…

Wata babbar kotu a jihar Legas da ke zamanta a Ikeja, ta yanke wa Sarkin Shangisha da ke yankin Karamar Hukumar Alimosho a jihar, Michael Mutiu Yusuf, hukuncin zaman kurkuku na shekara 15 bisa laifin yin garkuwa da kai.

An tisa keyar basaraken ne tare da wani mai suna Adams Opeyemi Mohammed da suka aikata laifin tare.

Sai dai kotun ta wanke matar sarkin, Abolanle, daga shari’ar bisa rashin samunta da hannu cikin badakalar.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hakeem Oshodi, ya yanke wa Sarkin hukuncin zaman kaso na shekara 10 ba tare da zabi ba kan laifin farko da kotu ta kama Sarkin da shi.

Sai kuma hukuncin zaman kurkuku na shekara daya ko zabin biyan N200,000 kan laifinsa na biyu.

Yayin da aka yanke masa zaman gidan yari na shekara 15 ba tare da zabi ba kan laifinsa na uku.

Yayin Shari’ar, Alkalin ya ce, “Na yarda da sassaucin da lauyan masu kare kansu ya nema, sai dai kotu ta lura babu alamar nadama a tattare da masu kare kan nasu.

“Hasali ma, mai kare kansa na farko ya yi kokarin ficewa daga kotun. Dole a koya masa hankali domin ya zama izina ga qasu,” inji shi.

Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa, a ranar biyar ga watan Yuli, 2017, Ogundare ya ce an yi garkuwa da shi ba don komai ba sai don ta da hankalin jama’a, wanda a cewar jami’in hakan ya saba wa sashe na 5 biyar na Dokar Haramcin Garkuwa ta 2017, mai lamba C17, ta jihar Legas.

Tun farko Sarkin ya rasa rawaninsa bayan da ‘yan sanda suka baje shi ga idon duniya daidai da abin da doka ta tanadar sakamakon laifin da ya aikata.