✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga karbar harajin ’yan kasuwa

Babbar kotun Jihar Kano ta dakatar da gwamnatin jihar daga karbar wasu kudaden haraji daga ’yan Kasuwar Sabon Gari har sai Kotun Koli ta yanke…

Babbar kotun Jihar Kano ta dakatar da gwamnatin jihar daga karbar wasu kudaden haraji daga ’yan Kasuwar Sabon Gari har sai Kotun Koli ta yanke hukunci.

Tun a zaman da ya gabata kotun ta ba da umarnin yin sulhu tsakanin ’yan kasuwar da hukumar kasuwar a madadin gwamnati, amma mahukuntan kasuwar suka ki yin sulhun.

Bayan nan ne mahukuntan kasuwar suka kara shigar da kara gaban Kotun Koli suna neman ta bar su, su ci gaba karbar kudaden.

A yau dai babbar kotun jihar karkashin jagorancin mai Shari’a Maryam Sabo ta dakatar da su daga karbar kudaden har sai Kotun Koli ta yanke hukunci.

Bayan fitowa daga kotun, lauyan ’yan kasuwar, Barrista Abdul’aziz Adam Muhammad, ya jaddada bukatarsu ta zuwa Kotun Koli wanda kuma kotun ta bayar da damar hakan.

Aminiya ta so ji daga bangaren lauyan gwamnati sai dai ba mu samu ji daga gareshi ba.

Tun a bara ne ’yan kasuwar suka shigar da mahukuntan kasuwar da Gwamnatin Jihar Kano kara kan zargin da da ’yan kasuwar ke yi cewa ana karbar musu kudaden haraji mara asali da kuma shirin kwace musu shagunan da suka gina bayan gobara a kasuwar.