✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da Ganduje daga gina shaguna a jikin wata makaranta

Kotun ta umarci gwamnatin da dakata har sai ta yanke hukunci

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako, ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano daga yunkurin da take yi na gina shaguna a jikin Makarantar Sakandiren Kwakwachi da ke Jihar.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Yusuf Ubale Muhammad, ta bayar da umarnin ne ranar Jumu’a.

Dakatarwar ta biyo bayan korafin da wasu mutane biyar suka shigar gabanta mai dauke da sa hannun daya daga cikinsu Nura Salisu Fagge inda suka nemi kotun da ta dakatar da yunkurin gwamnatin.

Sauran bangarorin da ake kara sun hada da Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar da Hukumar Tsara Birane ta Jihar (KNUPDA) da Ma’aikatar Kasa da Safiyo.

Lauyan masu kara, Barista Bashir Tudun Wuzurchi ya nemi kotun da ta dakatar da gwamnatin daga yunkurin nata.

Mai sharia Ubale Muhammad ya kuma umarci duka bangarorin biyu su dakata da gudanar da komai har sai sun saurare hukuncin karshe da za ta yanke, kamar yadda lauyan masu kara, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi ya nema.

Har ila yau, kotun ta dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2023.