✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bai wa Atiku da Obi damar bincikar kayayyakin zabe

Atiku da Obi sun tubure kan cewa su suka lashe zabe.

Kotun Daukaka Kara ta bai wa dan takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Labour, Peter Obi damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaben ranar 25 ga watan Fabarairu.

Tun farko ’yan takarar ne daban-daban suka mika bukatar neman a ba su damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a babban zaben 2023 tare da tilasta wa INEC ta ba su damar ganin kayan aikin da aka yi amfani da su a zaben Shugaban Kasar.

A ranar Laraba 1 ga watan Maris ne Atiku Abubakar ya shigar da tasa karar yayin da Peter Obi kuma ya shigar da tasa ranar Alhamis 2 ga watan nan na Maris.

Kan haka ne kotun ta umarci Hukumar Zabe ta bai wa dan takarar PDP damar duba kayayyakin zaben.

A yau Juma’a kuma kotun ta amsa bukatun ’yan takarar na duba kayan zaben sannan kuma su titsiye Hukumar Zabe kan wasu bayanai da za su bukata.

Kotun karkashin Mai Shari’a Joseph Ikyegh ta bayar da umarnin ne bayan da ta saurari wasu kararrakin da ’yan takarar biyu suka shigar tare da jam’iyyunsu.

PDP da LP wadanda a baya-bayan nan suka yi watsi da sakamakon zaben, sun ce samun damar ganin kayayyakin za ta taimaka musu a kalubalantar sakamakon zaben da suke yi wanda ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.

A cewar INEC, Tinubu ya ci zaben ne da kuri’u 8,794,726, inda Atiku Abubakar na PDP yake bi masa da kuri’u 6,984,520 sai Obi na Labour Party da ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.