✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu Ta Ba Da Umarnin Tsare Shugaban EFCC A Gidan Yari

Kotu ta umarci Shugaban ’Yan Sanda ya tisa keyar Abdulrasheed Bawa zuwa Gidan Yarin Kuje kan raina umarninta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya tabbatar da umarninta na tsare Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, a gidan yari kan raina umarninta.

Guda daga alkalan kotun, Chizoba Orji, ya ce yin watsi da umarnin kotun da Abddulrasheed Bawa ya yi, raini ne gare ta, don haka ta yanke masa hukuncin tsarewa a Gidan Yarin Kuje.

“Babban Sufetan ’Yan Sanda ya tabbatar da an bi wannan umarni sau da kafa, har sai Bawa ya gyara kuskurensa,” in ji alkalin.

To sai dai Shugaban EFCC din ya bayyana wa manema labarai cewa sun gama shiri domin daukaka kara.

Kazalika kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce Shugaban Rundunar  ba shi da masaniyar umarnin kotun.

Tun da fari dai kotun ta umarci EFCC da ta mayar wa tsohon Daraktan Ayyuka na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Vice Marshal Rufus Adeniyi Ojuawo, motarsa kirar Range Rover da tsabar kudi N40m, bayan gurfanar da shi da hukumar ta yi a gabanta a 2016.

EFCC na zargin sa ne da karbar N40m da motar daga wani kamfani mai suna Hima Aboubakar of Societe D’Equipment Internationaux Nigeria Limited ba bisa ka’ida ba.

Sai dai kotun ta wanke shi daga  zargin, ta bai wa EFCC din umarnin sakar masa kudin da motar, ita kuma ta ki bin umarnin.

 

Daga Idowu Isamotu  da Balarabe Alkassim da Rahima Shehu Dokaji