Yarinya mai shekara bakwai a wannan wata aka tabbatar mini tana da ciwon sikila. Shin ko za ta samu ta rabu da ciwon ganin ita karama ce? Kuma wadanne hanyoyi zan bi domin kula da lafiyarta?
Daga Musa A.D
Amsa: Eh a likitance in dai an tabbatar akwai ciwon sikila, to a yanzu dai akwai maganin waraka iri guda da muka sani, wato dashen sabon bargon kashi na wani marar ciwon ga ita mai ciwon, wanda muka taba ba da labari a nan cewa wadansu ’yan mata a shekarun baya sun je kasar waje an yi musu. Kamar yadda aka ce sun je kasar waje, hakan na nufin har yanzu ba a irin wannan tiyatar sauya bargon kashi a wannan kasa tukuna. Ko a kasar wajen ma ba kananan kudi za a kashe ba kafin a yi wa mutum tiyatar.
Hanyoyin kula da mai ciwon su ma suna da wahala sosai don haka sai ka daure, kuma sun hada da hana sauro taba yarinyar, wato duk dabarar da za ka yi kada ka rika bari sauro ya cije ta – akwai magunguna kuma da za a ba ta a asibiti domin taimaka wa kiyaye zazzabin cizon sauro da sauran cututtukan da kan saurin kama masu sikila. Haka kada ta rika shiga rana, don kada ruwan jikinta ya yi saurin karewa – ke nan sai ta rika yawan shan ruwa ko abu mai ruwa-ruwa koda a gida ne. Sa’annan duk ranar da ta tashi ta ce jikinta ba ya yi mata dadi, ko kai ka ga alamar ba lafiya ba, dole ne ka kai ta asibiti a tabbatar ba matsala.
Yaro ne yake yawan sambatu a cikin barci, har ta kai yakan yi da karfi a wasu lokuta. Shin wannan matsala ce?
Daga Alhaji Husaini Kura
Amsa: A’a a likitance ba matsala ba ce sambatu ko magagi ko murkashi a barci. A ido biyu ne sambantu kan zama matsala a likitance. A addinance dai mun san akan ce idan yaro na yawan yin wannan, kai ko ba ya yawan yi yana da kyau a yi masa addu’o’i kafin ya kwanta.
Amsar Malam Usama Mpape: Idan kana kusa ba za a maimaita tambayarka ba, amma amsarka ita ce cewa babu wasu adadin watanni idan ka fahimta.
Amsar Malama Safiya A.: Eh, ba dai magunguna ba, sai dai shawarwari da dama da ba za su zayyanu a nan ba, amma idan kuka daure kuka ga likitan/likitar mata ku duka na san za a samu warware matsalar da yardar Allah.
Amsar Malam Bashir Saleh: Abin yi a yanzu shi ne a jira sai bayan watanni shida a sake awon ciwon sanyin da na kanjamau din. Daga nan kuma idan sakamako ya fito kwa tambayi likitan asibitin da kuka yi gwajin shawarar yadda za a wanye.