✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko akwai matacciyar majina a jikinmu?

  Nusarwa: Wadansu za su iya fuskantar rashin jin dadin wannan karatu na yau musamman a tambayoyi biyu na farko, saboda cike suke da kalmomin…

 

Nusarwa: Wadansu za su iya fuskantar rashin jin dadin wannan karatu na yau musamman a tambayoyi biyu na farko, saboda cike suke da kalmomin da a al’ada kalmomi ne na ‘kazanta’. Amma da yake a aikin kiwon lafiya a wasu lokuta sai an hada irin wannan zance, bai kamata a ce ba za a amsa irinsu ba, domin mu ma’aikatan lafiya mun saba.

 

Wai shin da gaske ne akwai matacciyar majina a jikin mutum kamar yadda wadansu sukan fadi? Kuma yana da kyau a yi maganinta?

Daga Aminu Yakubu

Amsa: A’a sai dai a marasa lafiya saboda mu masu lafiya akwai majina a jikinmu mai aiki wadda ba matacciya ba, wadda ke aikin nade kwayoyin cuta daga hanci har zuwa huhu da aikin jika mana hanyoyin numfashi. Ita wannan idan ta bushe akan iya cewa ta zama tasono misali, amma ba wai ta mutu ba, za a ce ta bushe ne. Amma a marasa lafiya kamar masu shan sigari ko masu ciwon hanyoyin numfashi na COPD za a iya samun majinar da ta dade ba ta aiki amma jiki ya kasa fitar da ita. To wannan ita ce musabbabin matsalolin numfashin masu wannan matsala.

A masu lafiya ba sai an yi maganin majinar jiki ba, kamar yadda ka ce ka ji wadansu suna fadi, domin muna fitar da majina ko dai ta hanyar fyatowa ko ta kakowa ta hanyar tsane kanta-da-kanta, ko kuma ta hadiyewa, domin yawa-yawan majina ko mun so ko ba mu so ba, ko mun sani ko ba mu sani ba, ana hadiye su ne su bi bayan gida su fita, don haka ba sai an taya jiki aikin fitar da ita ba. Busassun na hanci su ne za a ga sai an fyato su da karfi kafin su fita. Kullum jiki na wannan aiki na sarrafa majina da fitar da ita, domin a rana jiki na sarrafawa da fitar da majina kusan lita guda daga jikinmu, wanda hakan kan karu zuwa lita daya da rabi zuwa lita biyu idan ana mura. Marasa lafiyar da aka yi bayani a sama su ne suke bukatar taimakon fitar da majina. Da fatan ka fahimci haka don ba a so a tsawaita bayani a kai.

 

Me ke kawo gyambo a kafafuwan mutane ya ki warkewa har sawun nasu ya kusa mutuwa, a zo ana neman yanke kafa?

Daga Umar Tsula Akuyam

Amsa: Manyan abubuwan da kan jawo gyambo a kafa su ne ciwon suga da ciwon sikila da sanyin kashi da ciwon kiba da ciwon jijiyoyin jini na kafa wato ciwon DbT. Za ka yi mamaki ba a ce jin rauni ke kawo ciwon gyambon kafa ba. Eh, haka ne domin mutanen da suke da lafiya da an yi rauni zai warke cikin ’yan kwanaki kadan, amma idan mutum yana da daya daga cikin wadancan cututtuka da aka lissafa a sama, idan ya ji rauni a kafa idan bai yi sa’a ba sai su zama gyambo wanda zai yi wata-da-watanni bai warke ba.

To wannan kin warkewar ce kan jawo raunin ya bazu ya kama jijiyoyin jini ya watsu. Idan ba a kula da ciwon ba har takan kai kafar ta fara rubewa sai an kai ga yankewa. Shi ya sa ake so duk masu irin wannan gyambo su daure su je asibiti inda tashi-guda dama kwanciya ce domin kula da ciwon har sai ya warke.

 

Zama wuri guda da masu shago kan yi na tsawon lokaci har awanni goma a wasu lokuta shin yana da illa ga lafiyarsu kuwa?

Daga Yusuf M.K da S. Makauraci

Amsa: Illa kai, ai ko kifi ma haka ya ce inji masu iya magana, wato ‘zama wuri daya tsautsayi.’ Mu ma a likitance haka ne, zama wuri daya na tsawon lokaci tsautsayi ne mai jawo ciwon kiba da ciwon zuciya da ma ciwon kafa na sanyin kashi da na jijiyoyin kafa wato ciwon DbT, saboda shi jiki ba a yi shi don zama ko kwanciya tsawon lokaci ba. Da mutum ya kwanta ko ya zauna tsawon lokaci shi a jikinsa ma zai fara jin kasala ta yi masa yawa. Idan ya ci gaba kuma nan da nan zai ga nauyinsa na karuwa, alamun ciwon kiba sun fara shiga. Don haka ke nan sai ana yi ana hadawa da zirga-zirga, misali duk bayan awoyi biyu a samu a tashi a motsa jiki na kamar minti 10.

 

Idan ciwon sanyi ya yi wa marainan mutum na bari guda illa, to dayan zai yi aiki ko kuwa sai an yi masa magani ko tiyata?

Daga Ibrahim A.

Amsa: Eh, haka ake fata, domin idan alamun ciwon sanyi suka kama maraina na bangare guda, ana kyautata zaton bai kama daya bangren ba, amma fa ba dole ba ne a ce shi ma na daya bangaren kalau yake ba. To da yake magungunan da akan bayar na sha ne, duk inda kwayoyin cutar suke a jiki zai bi ya kashe su, ana kyautata zaton ko da akwai a daya bangaren mai lafiya za su mutu. Illar ciwon sanyi ya kama maraina kamar a mace ne ya kama kwayayenta, wanda zai iya jawo rashin haihuwa. Don haka a wasu lokuta shi ma ciwon sanyi na maraina zai iya hana maza haihuwa idan ba a magance shi sosai ba. Ke nan watakila sai an ga mutum ya sake iya haihuwa, shi ne zai tabbatar su marainan masu lafiya ba su mutu ba.

 

Sai na ga wadansu suna zazzage magani mai kwanso wato kafso suna shanye garin. Shin shan magunguna masu kwanso na da illa ne?

Daga Hassan Ibrahim, Ningi

Amsa: A’a akasin haka ne, wato masu shan garin su bar kwanso su ne maganin ba zai wa tasiri ba, domin amfanin kwanson shi ne ya hana sinadarin acid na ciki narkar da maganin kafin ya bi uwar hanji. Don haka idan aka zazzage garin aka sha ruwan acid na ciki zai kashe karfin maganin, a zo ba a samu amfanin da ake nema ba.

 

Ina yawan shan danyen tumatir da sa man zaitun a abinci. Shin akwai matsala a haka ko babu?

Daga Sani Magama, Jibiya

Amsa: A’a ba matsala. Ai su kayan ganye da ’ya’yan itatuwa ba sa yi wa jikin mutum yawa.