✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko akwai bambancin ji a tsakanin ’yan Adam?

Ni dai yadda nake na kasance ba na son hayaniya. Ko kara aka yi sai na ji kamar a cikin kaina aka yi ta. Ko…

Ni dai yadda nake na kasance ba na son hayaniya. Ko kara aka yi sai na ji kamar a cikin kaina aka yi ta. Ko wace irin cuta ce haka?

Daga Aminu Danzomo, Jigawa

 

Amsa: Ba ciwo ba ne bambancin halitta ne. Ka san jinmu a tsakaninmu mu ’yan Adam yana bambanta daga wani zuwa wani, ko daga wani jinsi zuwa wani, ko daga babba zuwa yaro, inda a kimiyyance ake da ma’auni daga 20 zuwa 80 a tsakanin ’yan Adam, kuma duk wanda yake jin sauti a wannan tsakanin nasa daidai ne. Kai akwai ma bambanci daga dan Adam zuwa dabbobi, inda masana suka tabbatar dabbobi sun fi dan Adam karfin jin sauti. Akwai ma masu jin kasa da na mutane wato kasa da maki 20 a ma’aunin sauti.

Shi bambancin ji daga wani zuwa wani a tsakaninmu mutane ko babu ciwo ana samu, inda wadansu suka fi wadansu a cikinmu karfin ji, shi ya sa da an yi ihu zai shiga tsakar kan irin wadancan mutane. Wadansu kuma sai sun dauki shekaru a wuri mai kara, inda karar kan wuce maki 80 a ma’auin decibels, kamar a kamfani mai injuna masu kara ko situdiyo inda ake sa kade-kade masu karar gaske, ko yawan amfani da daga sautin kayan kunne na kida, sa’annan jinsu ke samun matsala. Matsalar da akan samu kuma yawanci ita ce cewa jinsu yakan ragu bayan wasu shekaru.

A tsakanin jinsi da jinsi kuma za ka iya ganewa idan misali ka zauna da Turawa. Za ka ga alama su Turawa da yawansu ba sa son kara ko hayaniya sosai ko miskala zarratin, domin abin na shigar musu kunne har tsakar kai. Ko watakila kai ma irinsu ne? Bambanci daga babba zuwa yaro shi ma akwai shi, inda akan ce yara sun fi manya ji mai nisan zango. Manya kuma sai wadanda suka fara tsufa ne jinsu yake raguwa ko sun yi aiki a wuri mai kara ko ba su yi.

Sai bambanci tsakaninmu da dabbobi. Akwai dabbobin da za su iya jin karar irin wadda ba ma iya ji, misali, wasunsu kan iya jin motsin jariri a cikin mahaifiyarsa (wato ultrasound) ko karar girgizar kasa na tsawon kilomitoci wanda dan Adam ba zai iya ji ba (wato infrasound).

Don haka ke nan ka ga ba duka aka taru aka zama daya ba, wato ba ciwo ba ne, bambancin halitta ne. Inda za a ce ciwo ne shi ne a zo a yi magana mai matsakaicin sauti a majalisi misali kowa ya ji abin da aka fada radau amma a ce kai ba ka ji ba. Ko kuma a ce kai sai an yi magana da karfi kafin ka ji.

 

Idan na kwanta barci da dare nakan ji fitsari. Idan na kyale ba zai dame ni ba sosai, idan kuma na yi to sai na yi kamar sau hudu ko biyar. Wannan ko matsala ce?

Daga Baba Gusau

 

Amsa: Kwarai matsala ce, musamman ma idan shekarunka sun ba 50 baya. Ana hasashen wata halitta ce a mafitsararka ta prostate ta kumbura take kawo maka irin wadannan alamu. Sai ka je an duba ko haka ne a wurin likitan mafitsara (urologist).

 

Ni kuma hancina ne yake yawan toshewa, idan ya saki daga baya ya sake toshewa. Shi ne nake neman shawara.

Daga Bashir A.

 

Amsa: Shawara ita ce ka samu likitan hancin ya leka hancin naka ya gani ko akwai abin da ke toshe maka shi. Babban abin da ya fi toshe hanci ban da mura shi ne tsiro, wato nasal poly.

 

Ina fama da olsa har tana hana ni barci. Shin olsa tana iya hana barci ne?

Daga Mujtaba Musa

 

Amsa: Kwarai kuwa akwai olsar iri biyu, akwai ta bangon ciki akwai ta farkon hanji. Ta farkon hanjin masana sun ce ita ce ta fi tashi da dare ta hana barci, har sai an ci ko an dan sha wani abu kafin ta yi sauki. Amma dai kullum muna nanatawa akwai maganin warkewa. Kawai dai sai aljihu ya motsa sosai ne, ita ce matsalar, domin magungunan masu karfi ne da tsada, ga kudin gwaje-gwaje. A mafi yawan lokuta magungunan lafawar ciwon kawai akan bayar, musamman idan ba a yi hoto an ga gyambon ba, amma idan marar lafiya ya nuna wa likita bukatar yana so a yi komai da komai har matsalar ta warke, to tabbas za a yi masa.

 

Idan hawan jini ya lafa idan aka auna za a ga alamar akwai ciwon?

Daga Mua’azzam Hassan

 

Amsa: Idan na fahimci tambayar kana tambaya ce ko idan mutum yana shan maganin hawan jini kuma maganin yana aiki hawan jinin ya sauka za a iya cewa ya warke? A’a idan mutum na da hawan jini kuma an tabbatar hawan jini ne, sai dai mu ce ciwon lafawa ya yi ba warkewa ba. Sai dai idan mutum gaba daya ya kawar da abin da ya kawo hawan jinin tunda farko, kamar misali idan kiba ce, a ce mutum ya rage kibarsa ya dawo daidai da sauran mutane, kuma hawan jinin ya tafi awon na tsawon watanni bai sake nunawa hawa ba, to a iya cewa ya warke. Sai a tsayar da magani a ci gaba da bibiyarsa na tsawon lokaci. Amma idan lafawa ya yi, ana iya rage maganin, ko a canja zuwa wani marar karfi misali.