✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Matafiya: Jirgi mai saukar ungulu zai fara shawagi a Jos

Za kuma a aika tawaga biyu ta ’yan sandan kwantar da tarzoma.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce za ta aika jirgi mai saukar ungulu da kuma tawaga biyu ta ’yan sandan kwantar da tarzoma birnin Jos da ke Jihar Filato domin tabbatar da tsaro.

Hakan na kunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Frank Mba ya aike wa manema labarai a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce Babban Sufeton ’yan sandan kasar, Usman Alkali Baba ya ce jirgin zai yi aikin tattara bayanai ne da kuma taimaka wa jami’anta da ke garin.

Kazalika sanarwar ta ce ’yan sanda sun kama karin mutum 13 da ake zargi da kashe wasu matafiya kimanin 30 ranar Asabar, inda suka zama 33 jimilla.

A Lahadin ta gabata ce IGP Alkali Baba ya bayar da umarnin tura tawagar ’yan sanda ta musamman domin kaddamar da bincike kan kashe matafiyan a Jos.

Matakamakin Sufeton ’Yan sanda, DIG Sanusi N. Lemu ne zai jagoranci tawagar da ta kunshi jami’ai daga bangarorin bincike da dama na rundunar.

Aminiya ta ruwaito cewa, maharan da ake zargi matasan kabilar Irigwe ne sun tare motocin matafiyan a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Jihar Ondo, bayan sun halaraci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a Jihar Bauchi.