✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kazamin fada ya barke kusa da Fadar Shugaban Kasar Sudan

Fadan safiyar Asabar na zuwa ne a yayin da Najeriya ke kokarin kwashe sauran ’yan Najeriya da suka rage a Khartoum.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, kazamin fada da makaman atilare ya bakre a kusa da Fadar Shugaban Kasar Sudan da ke birnin Khartoum.

Mayakan sa-kai na RSF sun yi ikirarin lalata motocin yaki ewa kwace makaman dakarun gwamnati da ke musu luguden wuta da jiragen yaki da kuma jirage marasa matuka.

An ci gaba da luguden wutan ne a safiyar Asabar ne a yayin da Ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan ke kokarin kwashe sauran ’yan Najeriya da suka rage a Khartoum.

Wani dalibin Najeriya da ke Khartoum ya shaiwa a Aminiya cewa a safiyar Asabar motoci sun zo jami’ar da suka taru somin kwashe su zuwa kasar Masar, inda daga nan za su hau jirgi zuwa gida Najeriya.

A yammacin Asabar, Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya a Ketare, Abike Dabiri-Erewa, ta wallafa wani bidiyo da  cewa, “Karin motocin ’yan Najeriya na hanyarsu ta zuwa kasar Masar, domin tasowa zuwa Najeriya,” tare da rokon a sanya su cikin addu’a. Sai dai kuma daga baya ta goge sakon.

Fadan na Asabar na zuwan ne duk da cewa a ranar Juma’a bangarorin da ke yakar juna ka shugabancin kasar sun amince su tsawaita tsagaita wuta da suka yi zuwa ranar Lahadi.

Baya ga sabon artabun na ranar Asabar a Khartoum, an yi ba-ta-kashi tsakanin bangarorin a biranen Bahri da kuma Ombdurman da yankunan kogunan Nil da kuma Dutsen Awliya.da ke makwabtaka da Khartoum.

Dauki-ba-dain ya haddasa rashin ruwa da abinci da wutar lantarki da sauran bukatu a birnin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kawo yanzu an kashe sama da 512 an jikkata wasu 4,200 kuma kusan kashi tara cikin 1o na asibitoci sun koma aiki jefe-jefi.

Rahoton majalisar dinkin duniyar ya ce yawan mutanen da abin ya shafa na iya karuwa, duk da cewa a halin yanzu a kwai mutum dubu 75 da ke zaman gudun hijira sakamakon rikicin.