✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kauyukan Neja 42 ne ke karkashin ikon Boko Haram’

Kalaman na zuwa ne kwana daya bayan Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya ce ’yan ta’addan sun kafa tutocinsu a wasu kauyukan jihar.

Dan majilasa mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas a Majalisar Dattijai, Sanata Sani Musa ya ce akalla kauyuka 42 ne a jihar suke karkashin kulawar kungiyar Boko Haram.

Rikicin dai ya yi sanadiyyar raba sama da mutane 5,000 da muhallansu a jihar cikin shekaru ukun da suka gabata.

Kalaman nasa dai na zuwa ne kwana daya bayan Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello shima ya ce ’yan ta’addan sun kafa tutocinsu a wasu kauyukan jihar.

Da yake magana a zauren Majalisar Dattijai ranar Talata yayin gabatar da wani kudiri kan kashe-kashen dake faruwa a Kananan Hukumomin Shiroro da Munya da Rafi na jihar, Sanata Sani ya ce sama da mutum 475 ne aka kashe a jihar daga watan Janairun bara zuwa yau.

Sanatan, wanda ya nuna takaicinsa kan karuwar hare-haren da ake kaiwa yankunan jihar, ya ce lamarin ya yi sanadiyyar kawo koma-bayanta kusan ta kowacce fuska, ba tare da hukumomi na daukar matakin da ya dace ba.

Ya ce, “Sun yi garkuwa da mutane da dama, sun kwace matansu tare da tilasta musu shiga Boko Haram. Sansanonin sojoji guda uku a Kananan Hukumomin Allawa da Bassa da Zagzaga yanzu duk an tashe su dungurungun, an kashe jami’an tsaro da dama sakamakon hare-haren.

“Zan iya tabbatar muku da cewa yanzu haka Boko Haram ta kafa tutoci a kauyuka da dama da suka kama, ciki har da Kaure da Allawa da Magami.

“Mazauna wadannan yankunan yanzu sun koma ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.

“Bugu da kari, yanzu haka makarantun Firamare a garuruwan Gwada da Kuta da Pandogari da Minna duk sun koma sansanonin ’gudunn hijira bayan an raba sama da mutum 5,600 da muhallansu a Kananan Hukumomin Shiroro da Munya a ’yan makonnin da suka gabata.

“Hakan dai na nufin matukar za su iya kaddamar da hare-hare a mazabar Neja ta Gabas, ban ga dalilin da za mu ci gaba da zama muna mike kafafunmu a Abuja ba,” inji shi.

A cewar Sanata Sani, tsakanin watan Maris na 2021 zuwa yanzu, ’yan ta’addan sun kashe sojoji 25, ’yan sanda da ma sauran jami’an tsaro, fararen hula 16 da ma wasu da dama da babu cikakkun alkalumansu.