✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen da za su yi Kamar Sallah ranar Asabar

Kasashe 14 da ba za su yi Karamar Sallah ba sai ranar Asabar

Kasashe goma sha hudu a duniya sun sanar cewa ranar Asabar za su gudanar da bikin Karamar Sallah a bana.

Hukumomin kasashen sun sanar da cewa Karamar Sallah ta kama ranar Asabar a kasashensu ne saboda ba a samu ganin sabon watan Shawwal ranar Alhamis a kasashen ba.

Kasashen su ne Iran da Libya da Pakistan da Oman da Japan da Malaysia da Indonesia da Brunei da Thailand da Singapore da  Australia da kuma Philippines.

A wannan karon dai akasarin kasashen duniya, ciki har da Najeriya da Saudiyya, sun yi Karamar Sallar ne a ranar Juma’a.

Sun yi Karamar Sallah a ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ne bayan a ranar Alhamis 29 ga watan Ramadan, an tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal — na karamar sallah — a kasashen.

Ana yin kamar sallah ne a duk ranar 1 ga watan Shawwal na kalandar Musulunci, mai kwanaki 29 ko 30 a wata, ya danganci lokacin da aka ga jinjirin wata.