✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashe 10 da ka iya lashe Gasar Kofin Duniya ta bana

Bayan lashe Gasar Kofin Duniya ta 2014, tawagar kwallon kafar Jamus ta gaza tabuka wani abun kirki.

A yanzu kidayar kwanakin da suka rage a soma Babbar Gasar Tamaula ta Duniya ta kare, inda tawagar kasashen duniya da suka yankin tikitin halartar gasar da za a fafata a Gabas ta Tsakiya sun hallara tare da zakakuran ’yan wasan da za su yi musu wakilci. 

A jiya Lahadi, 20 ga watan Nuwambar 2022 aka soma barje gumi a Gasar Kofin Duniya ta bana da Qatar ke karbar bakunci.

Faransa wadda ta lashe gasar a kasar Rasha a shekarar 2018, za ta yi kokarin kare kambunta, sai dai akwai kasashe da dama da za su yi kokarin kakkabo tawagar ta Les Bleus daga matakin.

Kasashe 32 ne za su kece raini a babban gasar kwallon kafa ta duniya, sai abin tambaya shi ne wacce kasa ce za ta bayar da mamakin cirar tuta a cikinsu?

Ga dai jerin kasashe 10 da ake hasashen za su iya kai bantensu a gasar:

10. Denmark

A halin yanzu dai Denmark ta nuna cewa karanta ya kai tsaiko, domin kuwa tana iya gogayyar kafada da kowace kasa.

Ana iya tuna bajintar da ta nuna a Gasar Euro 2020, duk da tsautsayin da ya auka wa hazikin dan wasanta Christian Eriksen.

A yanzu dai tawagar ta yi wa tauraron nata maraba wanda ya dawo da karsashi da kuma koshin lafiyar da zai iya taka rawar gani a Gasar Kofin Duniya ta 2020.

9. Belgium

Tawagar Belgium na daya daga cikin sahun kasashen da aka hasashen za su iya lashe Babbar Gasar Tamualar.

Wannan dai ba ya rasa nasaba da rawar da kasar ta taka na kare a mataki na uku da ta yi a Gasar Kofin Duniya ta 2018 da kuma bajintar da suka yi a Gasar UEFA Nations League.

8. Portugal

Portugal dai ta sha kashi a hannun Belgium a zagayen ’yan 16 na Gasar Euro 2020, lamarin da ya sa ta gaza kare kambunta a gasar.

Haka kuma, da kyar ta iya yankar tikitin zuwa Gasar Kofin Duniya ta Qatar a sakamakon ci 2-1 da tawagar Serbia ta yi mata wajen neman gurbi, inda sai da ta buga wasu wasannin sharar fage sannan ta iya fita kunya.

Sai dai ko shakka babu tawagar wadda Fernando Santos yake jagoranta za ta iya cirar tuta a babbar gasar la’akari da cewa tauraronta, Cristiano Ronaldo zai yi duk wata mai yiwuwa wajen ganin kasarsa ta yi nasara.

7. Netherlands

Bayan gaza kai bantenta na samun tikitin zuwa Gasar Euro 2016 da kuma Gasar Kofin Duniya ta 2018, tawagar ta Holland ta kai har zagayen ’yan 16 a Gasar Euro 2020. Sai dai ta je madakata yayin da tawagar Jamhuriyyar Czech ta taka mata burki.

Sai dai tawagar ta ci gaba da kwazo wanda ya nuna tana iya zama zakarar gwajin dafi a babban gasar ta bana.

6. Jamus

Bayan lashe Gasar Kofin Duniya ta 2014, tawagar kwallon kafar Jamus ta gaza tabuka wani abun kirki a tsawon shekaru hudu da suka biyo bayan nasararta.

Tun a matakin rukuni a koro tawagar daga Gasar Kofin Duniya ta 2018 karkashin jagorancin mai horaswa, Joachim Low.

A yanzu tawagar ta dawo kan ganiya tun bayan da ta Hansi Flick ya karbi ragamar horaswa, kuma ana kyautata zaton za ta fito kwanta da kwarkwata domin lashe Gasar Kofin Duniya ta 2022.

5. Sfaniya

Gasar Kofin Duniya ta 2018 ba ta zo da sa’a ba ga tawagar kwallon kafar Sfaniya. Kamar dai yadda ta kasance ga Jamus, ita ma tun a zagayen ’yan 16 aka fatattake ta daga gasar.

Sai dai a halin da ake ciki, yanzu tawagar ta tara zakakuran ’yan wasa masu jini a jika, wanda ya ba wa magoya bayan kasar kwarin gwiwar tabuka abun zo a gani.

4. Ingila

Har yanzu akwai Ingila ba ta murmure daga rashin nasarar da ta yi ba a wasan karshe na Gasar Euro 2020. Wannan dai na da nasaba ne da yadda  ’yan wasa da kasar baki daya suka ga samu suka ga rashi bayan sun kyallara idanu a kan lashe Gasar Euro karon farko a tarihi.

A yanzu ma dai ba ta baci ba don kuwa ana kyautata zaton tawagar za ta haska a Qatar duba da cewa ta tara zakukan ’yan wasa masu jini a jika.

3. Argentina

Gasar Kofin Duniya ta bana dai ita ce ta karshe da Lionel Messi zai buga kuma ita ce damarsa ta karshe na lashe kofin karon farko a tarihi bayan lashe gasar Copa America da ya yi a bara.

Tawagar ta Albiceleste ta yi bajinta wajen neman gurbi a Gasar Kofin Duniya ta 2022, duk da dai cewa tawagar Brazil ta fi ta haska wa wajen yankar tikitin.

2. Faransa

Faransa mai rike da Kofin Duniya tana kan gaba-gaba wajen sake lashe gasar a Qatar a bana. Ba abin mamaki ba ne ganin sunan tawagar a cikin mafi kyawun tawagai a duniya saboda tana da tarin taurari da babu shakka za su taka rawar gani.

Les Bleus ce ta lashe Gasar UEFA Nations League kuma tana cikin kasashe sahun farko da suka yankin tikitin Gasar Kofin Duniya ta Qatar 2022.

1. Brazil

Brazil wadda ta lashe Gasar Kofin Duniya sau biyar a tarihi, tana da tawaga mai karfin gaske ciki har da Neymar, Alisson, Richarlison da Philippe Coutinho hadi da ’yan wasa wadanda tauraruwarsu ke haskawa kuma suke kan ganiya kamar Vinicius Jr. da Gabriel Martinelli.

Ana hasashen tawagar ta za kawo karshen shekaru 20 da ta shafe ba tare da daga kofin ba wanda a shekarun farko-farko da soma gasar ta zama tamkar wata kwangiri karfen jirgi da ake yi wa kirari da gigun-gagun.