✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin 2023: El-Rufa’i ya ware wa matasa masu yi wa kasa hidima a Kaduna N300m

El-Rufa'i ya ce jihar za ta fara biyansu alawus a kowane wata

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce jihar ta ware kimanin Naira miliyan 300 a kasafin kudinta na 2023 domin matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC da aka tura jihar.

Gwamnan ya ce jihar za ta fara biyan matasan kudaden alawus-alawus a kowane wata, kari a kan wanda Gwamnatin Tarayya take ba matasan.

El-Rufa’i, wanda ya sami wakilcin Kwamishiniyar Bunkasa Walwalar Al’umma ta Jihar, Hajiya Hafsat Baba, ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan da bude ba da horo da matasan a sansanin NYSC na ba su horo a jihar ranar Talata.

Kwamishiniyar ta ce, “Gwamnatin Jihar Kaduna ta ware Naira miliyan 300 a kasafin kudinta na 2023 saboda matasa masu yi wa kasa hidima a jihar. Za a yi amfani da kudaden ne wajen biyansu alawus-alawus a kowane wata,” inji ta.

Kwamishiniyar ta kuma ce a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar, Gwamnan ya bayar da tabbacin kare lafiya da rayuwar matasan a matsayin abin da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kai.

Tun da farko, Shugaban NYSC a jihar, Odoba Abel Uche, ya ce sun kammala yi wa matasa 1,500 rajista a matsayin wadanda aka turo jihar a wannan karon.

Daga nan sai ya hore su da su kasance jakadun hukumar na gari a tsawon shekara dayan da za su shafe a jihar tare da kasancewa mutanen kirki kuma ’yan kishin kasa.