✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin kudin wuta: Kungiyar kwadago ta caccaki Gwamnati

Kungiyar Kwadato ta Najeriya (NLC) ta yi wa Gwamnatin Tarayya wankin babban bargo kan batun karin kudin wutar lantarki. NLC ta caccakin Gwamnatin ne bayan…

Kungiyar Kwadato ta Najeriya (NLC) ta yi wa Gwamnatin Tarayya wankin babban bargo kan batun karin kudin wutar lantarki.

NLC ta caccakin Gwamnatin ne bayan sanarwar da Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman ya fitar da ke cin karo da wadda Hukumar Wutar Lantarki (NERC) ta fitar da farko game da karin kudin wutar daga Naira biyu zuwa Naira hudu.

“Mun shigo wata shekara kuma da babbar abin da gwamnanti ta sa a gaba shi ne jefa yanayin tattalin ’yan kasa cikin mummunan kangi,” inji kungiyar.

Sanarwar da Shugaban NLC na Kasa, Ayuba Wabba, ta soki sanarwar  daMinistan ya fitar daga baya, mai karyata rahotannin da ke nuna an yi karin kudin.

Ayuba Wabba ya ce, tufka da warwarar da ke cikin sanarwan biyu, ya kara tabbatar wa ’yan Najeriya da fargabarsu ta cewa wahalar da suke ciki bata kare ba.