✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karashen Zabe: EFCC ta baza jami’anta 100 a Kano

EFCC ta ce za ta yi maganin masu shirin tafka magudi a zaben.

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta tura jami’anta 100 don yaki da sayen kuri’u a Kano, Katsina da kuma Jigawa a yayin karasa zaben da za a yi ranar Asabar a jihohin.

Kwamandan EFCC na shiyyar Kano, Farouk Dogondaji ne, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Kano a ranar Juma’a.

“Mun tura jami’ai 20 domin sanya ido kan yadda zaben ‘yan majalisar jiha zai gudana a Kafur da Kankara a Jihar Katsina,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa an kuma tura isassun ma’aikata domin sanya ido a mazabar Tudun Wada da Doguwa da Takai da kuma wasu mazabu na ‘yan majalisar jiha a Jihar Kano.

Dogondaji, ya ce an kuma tura wasu ma’aikata domin sa ido kan zabukan ‘yan majalisar dokoki a Katsina da Jigawa domin hana sayen kuri’u.

“Mun kuma tura jami’ai zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano domin sanya ido game da wadanda za su shigo jihar.

“Zamu fito fili a dukkan rumfunan zabe a Kano, Katsina da Jigawa domin sanya ido kan yadda za a gudanar da zabe da kuma bayan zabe.

“Za mu kasance a wurare tattara sakamakon zabe a kananan hukumomin da za a karasa zaben.

“Za mu yi hadin gwiwa tare da jami’an tsaro na jihar don samar da yanayi na lumana ga masu zabe,” in ji shi.

Ya ce tura jami’an na daga cikin kudirin hukumar na tabbatar da sahihin zabe a yankunan da za a karasa zaben.

Kwamandan, ya ce EFCC ta kuma dauki matakai, wadanda za su yi wahala ga wani mutum ko kungiya wajen yin magudi a zaben.

Dogondaji, ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su kasance masu kwazo da kwarewa wajen gudanar da aikinsu.”

Ya shawarci iyaye kan kada su bari a yi amfani da ’ya’yansu wajen aikata bangar siyasa, wanda a cewarsa duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a gaban kuliya.