✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Karancin mai na iya haifar da hauhawar farashin kayayyaki’

Hukumar ta ce karancin man fetur na iya jefa tattalin arzikin cikin matsala.

Hukumar Kididdigar ta Kasa (NBS), ta ce karancin man fetur din da ake fuskanta a fadin kasar na iya ta’azzara matsalar hauhawar farashin kayayyaki.

Mista Simon Harry, Shugaban hukumar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Talata, a wajen bayanna sakamakon kididdigar farashin kayayyaki ta watan Janairun 2022.

Simon ya ce matsalar za ta iya haifar da hauhawar farashin kayayyaki na wucin gadi, wanda hakan na iya girgiza tattalin arziki.

A cewarsa, “Ko muna so ko ba ma so, masu sufuri za su yi amfani da damar wajen kara kudin sufurin kayayyaki.

“Yanayin zai tilasta wa masu kayayyaki kara kudaden abubuwan da suke sayarwa.

“Don haka, wannan ba iya karin farashin kayayyaki zai tsaya ba, zai shafi tatalin arziki,” a cewarsa.

Kazalika, ya ce duk da irin rawar gani da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa ga tattalin arziki, hakan na iya shafar kasuwancinsu, wasu ma iya dakatar da ayyukansu na wucin gadi.

Sai dai ya ce ba za a iya yin harsashen hauhawar farashin kayayyaki a watan Fabrairu ba bisa la’akari da matsalar man fetur da ake fama da ita a halin yanzu domin ana ci gaba da tattara adadin.