✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karancin kudi: Da sauran rina a kaba — Masana

Ya kamata duk wani dan kasa ya tabbatar da cewa ya bude, tare da amfani da asusun banki.

Yayin da ’yan Najeriya ke kokawa kan wahalhalun rayuwa sakamakon karancin Naira, kwararru da masana harkokin kudi sun shawarci jama’a su jajirce domin tunkarar karin matsi da lamarin ya haifar saboda a cewarsu da sauran rina a kaba kafin a yi adabo da matsalar gaba daya.

Duk da tabbacin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar na saukaka matsalar karancin kudi a kasar nan, masana tattalin arziki da kwararru da masu sharhi kan harkokin kudi, sun cewa ’yan Najeriya za su ci gaba da rayuwa cikin karancin kudi na tsawon lokaci idan ba a samu manyan sauye-sauye kan yadda mahukuntan Bankin CBN suke tunkarar lamarin ba.

Idan za a tuna a makon jiya ne Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta tilasta wa CBN sauka daga dokin na ki, inda ta yi barazanar durkusar da tattalin arzikin kasar nan idan ba a samu ingantuwar zagayawar kudade a hannun jama’a ba.

Matakin ya zo ne bayan makonni da fara bin wani bangare na hukuncin Kotun Koli da ya tsawaita amfani da tsofaffin takardun kudin zuwa watan Disamban bana.

Sai dai wani abu da fito fili a karshen mako shi ne yawan kudin da bankunan suka samu ya yi matukar nesa da abin da tattalin arzikin kasa ke bukata domin yaukaka shi gaba daya.

Babu bankin da zai iya samar da rabin kudin da kwastomominsa ke nema— Manajojin bankuna

Wani babban ma’aikacin banki ya ce babu wani banki da zai iya biyan rabin bukatun abokan cinikinsa “Ba tare da ya shiga cikin babbar matsala ba.”

Sai dai kamar yadda wasu bayanai suka nuna, karancin kudin ya kara ta’azzara ne sakamakon yadda abokan huldarsu suke kauce wa kai ajiyar kudinsu a bankuna, hakan ya tilasta yawancin rassan bankunan dogaro da manyan ofisoshinsu na shiyya.

Kuma a nasu bangaren, manyan ofisoshin suke dogara ga CBN kadai don samun takardun kudi a makonni biyu da suka gabata, saboda kudaden da suka rage a rumbunansu sun kare, bayan tattara tsofaffin takardun kudin a watan Janairu da Fabrairu.

“Tsarin ba mai dorewa ba ne, kuma ban ga wani abu da wani zai yi don kawo karshen matsalar samar da tsabar kudi ba sai tsarin ya canza.

“Idan abokan hulda za su cire tsabar kudi kawai da zimmar adana wani bangare na kudin kuma babu wanda zai mayar da abin da ya amsa zuwa bankuna a matsayin ajiya; to nawa ne CBN zai buga domin samar da tsabar kudin da za su wadatar a hada-hadar yau da kullum?,” wani ma’aikacin banki ya tambaya.

Aminiya ta gano cewa idan ba a dauki tsauraran matakai ba, bankuna na iya fuskantar rashin kudi gaba daya yayin da hada-hadar kudi ta koma kamar baya.

A wasu lokuta, alal misali, katunan ATM din wasu bankuna kan takaita wa masu hada-hada cirar Naira dubu biyu kacal ne a lokaci guda kamar yadda yawancin injinan ATM ba sa biyan fiye da Naira dubu 20 a kowace rana.

Sannan Gwamnan Bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bukaci ’yan Najeriya su kara kaimi wajen tunkarar tsarin na Kashles, yana mai cewa kasar nan ba za ta koma kan tsarin dauri na gabanin sake fasalin Naira da bankin ya yi ba.

Idan Gwamnan ya canza matsayinsa, bayanai ba su nuna haka ba.

Misali, kudaden da suke zagawa a hannun jama’a, sun ragu daga Naira tiriliyan 3.292 a karshen bara zuwa Naira biliyan 982 a karshen watan Fabrairu.

Wannan na nufin, kimar ta fadi da kashi 70 cikin 100 a cikin wata biyu.

Lallai ne CBN ya kara kudaden da ke yawo zuwa Naira tiriliyan 2 — Kwararre

A hirarsa da Aminiya, Farfesa Garba Ibrahim Sheka na Sashen Tsimi da Tanadi na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya alakanta matsalar takardun kudin kan abubuwa uku: raina Kotun Koli da CBN ya yi da zakkewar da CBN wajen lallai sai an koma tsarin Kashles; sannan yadda babban bankin ya ce ya lalata tsofaffin kudin da ya amsa daga hannun jama’a.

Ya ce batun gaskiya CBN ba ya da isassun takardun kudin da zai rarraba wa jama’a, saboda shirinsa na mayar da kaso uku cikin biyar na kudaden zuwa tsarin Kashles.

Ya ce: “Raina kotu babbar illa ce a kasa, ta ba da umarni a ki bi.

“Babban Bankin Kasa ya yi biris da umarnin kamar ba doka ce ta kafa shi ba.

“Sannan nacewar da suka yi cewa dole sai an bi Kashles din, dama abin da suka yi niyya kaso biyar na kudin da ke yawo su rike kaso uku.

“Sun lalata kudaden nan, muna da cikakkiyar shaidar sun yi haka.”

Ya ce, “Matsalar tsaro ce ma ta taimake mu, in ba domin haka ba da ba za a samu tsofaffin kudin ba gaba daya.

“Matsalar tsaro ta sa sai dai su yi ta yanyanka kudin maimakon zuwa daji a kone su -wanda hakan yakan dauki lokaci.

“Amma da sun samu damar fita daji don kone su; to kuwa da sun kone kudin gaba daya.

“Ana tsoron haduwa da masu garkuwa da mutane da suke neman miliyoyin Naira sannan ga kudade nan ana so a kone su, ka ga in suka kawo hari sai dai su kwasa kawai.”

Farfesan ya soki CBN na ko ta halin kaka sai an yi aiki da tsarin Kashles, inda ya ce Najeriya ba ta kai lokacin dabbaka tsarin yadda ya dace ba, yana mai kwatanta shi da rashin hankali.

“Netwok da bankuna suke amfani da shi ba ya da karfi. Ana ji ana gani mutum yana son tura kudi sai su ki tafiya.

“Kamar yadda aka fada a Kano, a kananan hukumomi 44, kusan 24 ba su da ma netwok din gaba daya; amma duk da haka an dage sai an yi tsarin. Rashin hankali ne kawai,’’ in ji shi.

Ya kara shaida wa Aminiya cewa, a yadda lamura suke tafiya yanzu, ba ya hangen shawo kan matsalar karancin kudin har zuwa karshen bana.

“In da buga sababbin kudin ake yi da yanzu sun wadata,’’ in ji shi.

Ya ce, biliyoyin kudin da ake cewa ana kashewa wajen buga kudaden abin kamar al’amara.

Sai dai ya ce tsarin na Kashles yana da tasa fa’idar kamar zabtare hauhawar farashi wanda karancin kudi a hannun jama’a zai taimaka wa hakan.

Aminiya ta tambayi Farfesan kan mene ne dalilin da yake gani abokan huldar suke kin kai kudinsu ajiya a bankuna, inda ya ce suna gudun wulakanci ne.

“Kai da kudinka sai ka kwana da yunwa ko jarinka ya karye; ka zama talaka. Sannan ga fargabar da mutane suke yi kan tsare-tsaren da gwamnati take bullo da su.

“Amma dai abu ne mai kyau ajiye kudi a banki domin zagayawar kudi shi ne ci gaban tattalin arziki.

“Idan akwai isassun kudade a banki, za a samu a zuba jari a harkar noma ko masana’antu.

“Zagayawar kudi shi ne bunkasar tattalin arziki. Kawai dai hukumomi su tabbatar wa jama’a samun kudinsu a kowane lokaci suka bukata a banki,” in ji shi.

A ganin Dokta Abubakar Muhammad Sa’idu Dukku, kwararre a harkar tattalin arziki a Jihar Gombe, a yanzu an samu wadatar kudi a hannun jama’a don haka da wahala a ci gaba da fuskantar matsalar karancin kudin, saboda jama’a sun daina kai kudi banki maimakon hakan sai dai karbar kudin daga bankuna.

Ya ce, “Hakan ya sa kudaden da suke yawo a tsakanin mutane sun yawaita.

“Yanzu za ka fid da kudi cikin sauki a wuraren PoS da ATM da sauran wuraren hada-hada. Ina ganin da wahala a sake komawa gidan jiya.”

Sai dai ya yarda cewa karancin kudi a farkon lamari ya haifar da nakasu ga tattalin arziki, “Saye da sayarwa sun samu nakasu.

“Darajar kaya ta yi ta karyewa. A yankunan karkara, za ka iske mai kaya ya ce maka ba ya bukatar taransifa, kudi a hannu yake so, wannan ya sa kayayyaki suka yi ta karyewa ainun.

“Wannan ne babbar illar da tsarin Kashles ya haifar,” in ji shi.

Ya amince cewa Najeriya ba ta kai lokacin yin hijira kacokan zuwa ga tsarin Kashles ba.

Ya yi kira ga Bankin CBN ya kara buga sababbin takardun kudi kuma ya kara sake kudaden da za su yi yawo a hannun jama’a.

“Kafin a dawo da amfani da tsofaffin takardun kudin, masana sun ce CBN ya tattara kimanin Naira tiriliyan uku daga bankuna da hannun mutane.

“Amma abin mamaki alkaluma sun nuna CBN ya buga sababbin kudin da ba su wuce Naira biliyan 500 ba, wanda daya bisa shida ke nan na abin da ya tattara.

“Abin da masana suka ba da shawara don kawo karshen karancin kudin shi ne idan CBN ya tattara Naira tiriliyan uku ya kamata akalla ya buga Naira tiriliyan biyu wato biyu bisa uku na abin da aka karbe; in ya so kashi daya bisa uku ya zama Kashles.

Hanyar da CBN ya kamata ya bi ke nan don kawo karshen matsalar,’’ in ji shi.

Marubuci, kuma mai fashin baki kan tattalin arziki a Abuja, Jameel Muhammad Dahiru ya ce, rashin kudi a hannun mutane, matsala ce ta harkokin tattalin arziki.

“Shi CBN, ba ya janye Naira tiriliyan 3.2 don ya sake dawo da adadin ba ne.

“Ya janye adadin ne don kudin da suke yawo a hannun jama’a sun yi yawa, wanda ya kawo hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni.”

Shi ma ya yi ittifiki da sauran masanan cewa ya dace CBN ya dawo da kudin da suke yawo zuwa Naira tiriliyan biyu, wanda wannan adadin shi ne zai wadatar a gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da an samu hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni ba.

“Domin haka, karancin kudi a hannun mutane zai ci gaba kadan kafin mu samu bakin zaren.

“An riga an yi bari, ba kuma za a kwashe duka ba,’’ in ji shi.

Ya ce ya dace ’yan Najeriya su rungumi tsarin na Kashles, inda ya ce ko ba jima, ko ba dade, dole ne za a tsunduma cikin tsarin, saboda tsari ne na duniya.

“Shiga wannan tsari ya zama dole, in dai muna son ci gaban tattalin arzikin kasarmu da kuma rage almundahana da sata da cin hanci a harkokinmu na yau da kullum da ake amfani da kudi.

“Ya kamata CBN da sauran kafofin gwamnati, su fito da tsarin ilimantar da talaka kan manufa da alfanun shiga tsarin na Kashles.

“Sannan gwamnati ta fito da wasu jerin tsare-tsare da za su rage wa talaka radadin shiga tsarin.

Ya ce, “Na daya, ya kamata duk wani dan kasa ya tabbatar da cewa ya bude, tare da amfani da asusun banki.

“Na biyu, ya kamata talaka ya rage burin aikin gwamnati. Sana’o’i na ayyukan kai sun fi wanzar da riba da wadata a cikin jama’a, fiye da aikin gwamnati.

“Gwamnati ta fi karfi ne wajen tsare-tsaren gudanarwa da kafa dokoki.

“Na uku, ya kamata talaka ya yi kokarin rungumar noman zamani, wanda shi ya fi kawo riba da ci gaban tattalin arziki,” in ji shi,

Masanin ya ce matsalar ilimi da tsarin gudanarwa da na na’urori su ke sa jama’a dari-darin kai ajiyar tsabar kudinsu a bankuna.

“Duk mai asusun ajiya a banki, yana bukatar wayar salula da kuma Intanet.

“Yawancin talakawanmu, suna da karancin hulda da abubuwa ukun nan.

“Wannan yana faruwa ne saboda talaka bai daga yanayin kansa ya kai ga wannan matsayi ba, ko kuma domin gwamnati ba ta wadatar da wadannan kayayyaki ba,” in ji shi.