✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karancin dala: Sri Lanka za ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya

Sri Lanka za ta rufe ofishin jakadancinta karancin dalar Amurka a Najeriya.

Sri Lanka za ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya saboda ta rage kashe kudin gudanarwa da kuma adana dalar Amurka da take matukar bukata a halin yanzu.

BBC ya ruwaito Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar tana cewa za ta rufe babban ofishin jakadancinta a Najeriya sannan ta rufe wasu kanana a Jamus da Cyprus.

A zantawarsa da jaridar Daily Mirror, Ministan Harkokin Wajen Sri Lanka, Farfesa Gamini Lakshman Peiris ya ce kasarsa za ta mayar da ayyukan ofishin jakadancinta da ke Frankfurt a Jamus zuwa birnin Berlin.

Ya ce ofishin jakadancinta na Najeriya zai kuma ci gaba da aiki ta hannun ofishin jakadancinta da ke kasar Masar.

A makon jiya ne Majalisar Ministoci ta tattauna kan karancin dalar Amurka da kuma matsin tattalin arziki da ta fuskanta a rubu’i na uku na bana, lamarin da ya sanya ta shimfida matakan da za a bi domin tufkar hanci.

Ana iya tuna cewa, a shekarar 2017 ne Najerita ta rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Colomba a Sri Lanka, matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai sake duba shi.