✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Kotu ta sassauta sharudan bayar da belin Muhuyi Magaji

Matakin ya biyo bukatar da lauyoyinsa suka shigar a gaban kotun

Kotun Majistare mai lamba 58 a Jihar Kano ta sassauta sharuddan bayar da belin da ta sanya tun da farko ga tsohon Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Hana Karbar Rashawa ta Jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Kotun, wacce ke karkashin Mai Shari’a Aminu Gabari, dai ta ya ke hukuncin ne yayin zamanta na ranar Laraba.

Ana dai zargin Muhuyi da laifin bayar da rahoton karya, laifin da ya saba da sashe na 140 na Kundin Penal Code.

Kotun ta dauki mataki ne biyo bayan rokon da lauyan wanda ake zargi, Barista Muhammad Danazumi ya yi a gaban kotun.

Idan za a iya tunawa a ranar 29 ga watan Afrilun 2022, Mai Shari’a Aminu Gabari ya sanya N500,000 a matsayin kudin ajiya tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Mutum na farko a cewar kotun dole ya kasance mahaifin wanda ake tuhumar ko kawunsa wanda kuma zai gabatar da takardun harajinsa na shekaru uku ko kuma ya ajiye fasfo dinsa.

Mutum na biyu kuma zai zama Limamin  Masallachin Juma’a na unguwar Ja’en da ke birnin Kano ko kuma dagacin unguwar.

A cikin takardar rokon mai shafi 11, ta bayyana cewa mahaifin wanda ake zargin ya rasu.

Haka ka sun shaidawa kotun cewa wanda ake karar mutum ne Mai kima a cikin a’lumma haka kuma lauya ne.

“Laifin da ake zargin sa da shi laifi ne da za a iya bayar da belin idan kuma har aka sami mutum da laifin aikatawa, to zai wuce a daure shi tsawon shekara guda ba ko kuma biyan kudin diyya na fam 20 ko kuma a hada dukkanin biyu,” inji takardar.

Lauyan ya kuma ce a karkashin sashe na 173 na Kundin laifufuka na Jihar Kano na ACJL, wajibi ne a bayar da belin wanda ake tuhuma matukar hukuncin laifinsa bai kai hukuncin shekara uku ba.

Sai dai a takardar rokon da take suka ga ta wanda ake kara, mai gabatar da kara Barista Wada A. Wada, ya nemi kotu da ta yi watsi da mutanen da Muhuyi ya gabatar a matsayin masu tsaya masa saboda ba su cancanta ba.

Ya kuma bayyana wa kotun cewa wanda ake kara bai cika sharudan belin da aka sanya masa ba, da zai sa ya samu ya fita daga gidan gyaran hali.

A yayin yanke hukuncin, Alkalin Aminu Gabari ya bayyana cewa alkali yana da damar sanya oda ko kuma ya soke ta.

“Kotu ta bayar da oda cewa wanda ake kara zai iya gabatar da dan uwansa a maimakon mahaifinsa ko kawunsa su tsaya masa,” inji alkalin.

Haka kuma kotun ta ce zai iya gabatar da duk wani babban mutum a cikin al’umma a maimakon limamin Masallachin Juma’a na Ja’en ko Dagacin unguwar.

Sai dai Alkalin ya ce sauran sharuddan belin suna nan kamar yadda suke tun farko.

Daga nan sai ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Mayun 2022 don sauraren shaidu.